
Kungiyar Kiristocin Najeriya ta ce bata yadda ba kuma ta yi Allah wadai da kulle makarantu da jihohin Bauchi, Katsina, Kano, da Kebbi suka yi saboda zuwan Ramadana.
A sanarwar da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ya bayyana cewa wannan mataki zai kawo koma baya ga ci gaban ilimi da hadin kai a Najeriya.
Kungiyar tace kulle makarantun zai taba harkar ilimi wadda ‘yanci ne na dan adam kuma sannan ginshiki ne na ci gaban al’umma kuma hakan zai kara tabbatar da koma baya ga harkar ilimi a jihohin.
Yace ba’a tuntubesu dan neman shawara kamin daukar wannan mataki ba kasancewa akwai kiristoci a wadanan jihohin.
Yace kuma wani abin mamaki shine kasashen da musulmai suka fi yawa irin su UAE, da Saudi Arabia da sauransu duk basu kulle makarantu ba saidai sun rage yawan lokacin da ake yi a makarantun saboda zuwa watan Ramadana.
Yace an haka idan Gwamnonin wadannan jihohi basu dauki mataki ba zasu shiga kotu.