
Ministar Al’adu, Hannatu Musawa ta bayyana cewa dan kudu take son ya zama shugaban kasa a shekarar 2027.
Ta bayyana cewa, hakan zai sa a samu adalci tunda Dan Arewa yayi shekarau 8 yana mulki.
Hannatu ta bayyana hakane a hirar da aka yi da ita a gidan Talabijin na Channels TV.
Tace tana fatan nan gaba za’a daina maganar karba-karba a rika baiwa wanda ya dace kawai mulki.