Dan gwagwarmaya kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa bai taba ganin mutane a cikin tsananin yunwa irin ta zamanin mulkin Tinubu ba.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Sahara Reporters.
Yace Gwamnatin Tinubu ta yi alkawarin idan ta cire tallafin man fetur, zata yi amfani da kudin wajan gina kasa da ayyukan ci gaba.
yace bai dade da dawowa daga jiharsa ta Asaliba, jihar Ondo amma bai ga wani abin ci gaba ba da aka gina. Yace rabon da ya ga lalataccen titi irin wanda ya gani an dade.