Friday, January 16
Shadow

Ji yanda wani yayi barazabar kulle asusun ajiyarsa da bankin Ja’iz saboda bankin basu tura masa sakon taya Maulidi ba, yace abin takaici shine sauran bankunan da bana Musulunci ba sun tura masa sakon taya murnar Maulidi amma banda Ja’iz

An samu suka ga bankin Ja’iz wanda na Musulunci ne saboda kin aikawa masu hulda dashi sakon taya murnar Maulidi.

Wani da yayi korafi akan hakan yace abin takaici shine bankunan da bana Musulunci ba sun aikawa musulmai sakon taya Murnar maulidi.

Amma bankin na Ja’iz wanda yake ikirarin na musulmai ne be aika sakon taya murnar maulidi ba.

Wasu dai sun yi barazanar daina hulda da bankin na Ja’iz.

https://twitter.com/YasinAwwal/status/1963956368240472256?t=zQVGOFHNEJWptVtY47lffw&s=19

Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad shima ya tabbatar da hakan inda yace shima ya lura bankin na Ja’iz basu tura sakon taya Maulidi ba.

Wasu dai na alakanta bankin da cewa ba Izala ne shiyasa hakan ta faru.

Karanta Wannan  Abin takaici, Kasar China ce kadai cikin kasashen Duniya ta nuna da gaske tana tare da Najeriya tun bayan Bharazanar Amurka

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *