Sunday, January 19
Shadow

Banson kasata Ingila ta zama kamar matalauciyar kasa Najeriya>>Inji Kemi Badenoch

Shugabar Jam’iyyar ‘yan ra’ayin mazan jiya ta kasar Ingila, UK Conservative Party, Kemi Badenoch ta sake sukar ‘yan Najeriya duk da cewa ita ‘yar asalin Najeriyar ce.

Da take magana ta farko a shekarar 2025 a wajan wani taro na musamman ranar Alhamis, Kemi tace bata son ingila ta zama kamar Najeriya, tace ta ga yanda danginta masu hali suka tsiyace saboda rashin gwamnati me kyau da tsadar rayuwa da ta yi yawa.

Kemi na ‘yar shekaru 16 ta bar Najeriya zuwa kasar Ingila da kudin babanta na karshe wanda basu wuce fan £100 ba.

Kemi ta kara da cewa, tana aiki tukuru domin ganin wahalar da ke Najeriya bata maimaitu a kasar Ingila ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Dan takarar gwamnan jihar Edo yana cewa zasu samarwa jihar matsalar tsaro

A baya, Kemi ta zagi ‘yan Najeriya da cewa ‘yan fashi da makami ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *