Saturday, April 11
Shadow

Bayan da aka shafe kwana da kwanaki ana neman matar auren nan, a karshe dai an iske ta a dakin Otal ita da Qartonta suna shakatawa

Wata matar aure me suna Mrs Tilewa Olatunde Funke ‘yar kimanin shekaru 42 ta bace ana ta nemanta.

Lamarin ya farune a garin Ilara-Mokin na jihar Ondo.

Saidai da bincike ya tsananta, ‘yan sanda sun ganota a dakin otal da wani me suna Isa Alaba dan kimanin shekaru 55 a dakin otal suna shakatawa.

Hukumar ‘Yansandan ta bayyana cewa matar da kanta ta kai kanta wajan mutumin ba garkuwa yayi da ita ba kuma an warware matsalar cikin ruwan sanyi.

Hukumar ‘Yansandan ta yi kira ga mutane dasu daina yada labaran da basu inganta ba kan lamarin.

Karanta Wannan  Kalli Cikakken Bidiyon hirar da BBChausa ta yi da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *