
Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa, Gwamnatin jihar ta mayar da malamin Makaranta, Abduljalal Usman bakin aikinsa bayan da suka ta yi yawa a kafafen sadarwa.
Da farko dai an dakatar da Abduljalal Usman ne na tsawon watanni 3 babu Albashi bayan da ya fito yayi korafin cewa bai gode da tallafin abinci sa’i daya na Shinkafa da Masara ba da aka bashi.
Bidiyon nasa ya watsu a kafafen sada zumunta sosai.
Hakan yasa aka dakatar dashi.
Saidai bayan hakan an yi Allah wadai da lamarin, abinda yasa aka mayar dashi bakin aikinsa kenan inda hukumar tace za’a ci gaba da bincike kan abinda ya aikata.

Shahararren dan kasuwa na jihar kaduna, Mahdi Shehu ya aikawa Abduljalal Usman tallafin Naira 120,000 sannan ya ce masa idan dai wannan lamari yasa aka koreshi daga aiki, yayi masa alkawarin aiki.
Sannan yace ba sai ya bar jihar Kebbi ba, ya zabi makaranta da zai rika koyarwa shi kuma zai rika masa albashi har iya tsawon rayuwarsa.
Mahdi Shehu yace yayi bincike ya gano cewa, Abduljalal Usman Albashin Naira 35,000 ake biyansa