
A karshe dai, Shugaban Kungiyar daliban Najeriya, Atiku Abubakar Isah ya fito ya wanke dan shugaban kasa, Seyi Tinubu kan zarge-zargen da ya masa.
A baya dai An ga Bidiyon Atiku yana cewa Seyi Tinubu ya masa tayin karbar Naira Miliyan 100 dan ya goyi bayan babansa, Bola Ahmad Tinubu.
Yace amma yaki amincewa shine Seyi Tinubun ya dauki nauyin ‘yan daba suka lakada masa duka.
Saidai bayan wannan zarge-zargen ne hukumar ‘yansandan farin kasa, DSS suka kama shugaban daliban, kamar yanda kafar Sahara reporters ta ruwaito, inda aka tursasashi ya karyata kansa game da zargin da yawa dan shugaban kasar.
A karshe dai Atiku ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa duk abinda ya fada, abokin takararsa me suna Ladoja Olusola ne ya rika gaya masa dan ya masa barazana.