
Babban Sifeton Ƴansandan Najeriya, Kayode egbetokun ya naɗa CSP Benjamin Hundeyin a matsayin sabon mai magana da yawun rundunar ƴansandan ƙasar (FPRO)
Naɗin Hundeyin na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado, Muyiwa Adejobi ya fitar.
”Babban Sifeton ƴansandan ya buƙace shi da aiki da ƙwarewarsa ta sadarwa wajen inganta aikin ɗansanda a Najeriya ta hanyar ƙarfafa hulda da jama’a,” in ji sanarwar.
Kafin sabon muƙamin, CSP Benjamin Hundeyin ya kasamnce kakain rundunar ƴansanda reshen jihar Legas, inda ya kwashe shekaru yana wannan aiki.