Shugaba Biden na Amurka ya yi kira ga Isra’ila da Hamas su amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita a yakin da suke yi tsakaninsu.
Yarjejeniyar za ta sa jami’an Isra’ila su tsagaita wuta ta tsawon mako shida, sannan Hamas ta saki Isra’ilawan da ta yi garkuwa da su – a kuma saki Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen yari a Isra’ila.
Yarjejeniyar ta yi tanadin Isra’ila za ta janye daga yankunan Gaza sannan ta kyale a rika shiga da kayayyakin agaji.
Yayin da za a a ci gaba da tattaunawa, yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki har a kai ga sakin duka wadanda aka yi garkuwa da su.
Daga nan dakarun Isra’ila su fice daga Gaza Falasdinawa su koma gidajensu su ci gaba da rayuwa.