
Wani Bidiyo da ya nuna yanda wasu ke hada manja ta hanyar kara masa kala dan yayi jaa sosai a kudancin Najeriya ya jawo cece-kuce sosai.
Bidiyon ya dagawa mutane hankali sosai inda aka rika kiran gwamnati ta dauki mataki kan lamarin.
An yi kira ga hukumar NAFDAC da su tsaurara bincike kan lamarin dan daukar matakan da suka dace.