
Shahararriyar ‘yar Shi’a me yin Tiktok Fatima Saeed ta mayarwa ‘yan Iazala da ‘yan Salaf masu kallon ‘yan Shi’a da ‘yan darika a matsayin ‘yan wuta martani.
Ta bayyana cewa abin dariyane wai suna tunanin idan aka je Lahira cewa za’a yi su shiga Aljannah amma ‘yan Shi’a da ‘yan darika su shiga wuta.
Tace tana Alfahari da Shi’a kuma tasan duk imanin da aka dasashi tare da son iyalib manzon Allah ba zai tabe ba.
Fatima dai kan sha mayar da martani ga masu sukarta saboda bin akidar Shi”a.