
Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi sun fara yin zabe dan yi mata kiranye ta dawo daga wakiltarsu da take a majalisar Dattijai.
Bidiyo ya nuna yanda tuni aka fara kada kuri’a dan yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye.
Sanata Natasha Akpoti dai ta zargi kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da nemanta da lalata zargin da ya karyata.
Dalilin haka aka dakatar da ita daga ayyukan majalisar na tsawon watanni 6.