Tauraron Tiktok kuma mawaki, G-Fresh Al’amin ya bayyana cewa me masa bidiyo ne ya tura ‘yan Hisbah Gidansa.
G-Fresh dai ya bayyana hakane a shafinsa cikin wani bidiyo daya wallafa a Tiktok.
Ya bayyana cewa, me masa Bidiyo ne ya ci amanarsa kuma ya kammala bincikensa babu wanda zai gaya masa akasin haka.
A baya dai, Hisbah ta kama G-Fresh Al’amin inda aka yi masa nasiha tare da sakashi a Islamiya.