Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta sanar da kama wani mutum da ya hadiyi kwayoyi dan ya kaisu zuwa kasar Faransa.
Mutumin an kamashi ne a filin jirgin saman Abuja yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa birnin Paris, babban birnin kasar Faransa.
Yace an bashi kwayarne ya kaiwa wani inda aka masa alkawarin bashi Euro Dubu 3.