
Sanata Ali Ndume yayi zargin cewa, na kusa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna neman a basu kudi, cin hanci kamin su bari mutum ya samu damar ganin shugaban kasar.
Ali Ndume ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Arise TV inda yace wasu kalilan ne suke samun damar ganin shugaban kasar ba tare da shamaki ba.
Ndume yace yakan ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne kawai a wajan taro.