Hukuncin Kotu yasa murna ta barke a fadar Nasarawa inda Sarki Aminu Ado Bayero yake.
An ga matasa na buga wutar murna inda suke nuna cewa sune suka yi nasara a kotu:
Kano dai ta dauki dumi inda kowace bangare tsakanin na Sarki Muhammad Sanusi II da na Sarki Aminu Ado Bayero ke cewa shine yayi nasara a kotun.