
Wani Bidiyo da Dan Bello yayi ya dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan da ya bankado badakalar aikin Titin Legos zuwa Calabar.
Dan Bello yace shekaru 2 ana aikin titin amma har yanzu bai wuce Kilometre 50 ba, har yanzu ba’a ma fita daga lagos ba.
Sannan yace Titin yanzu haka har ya fara lalacewa sannan ya toshe hanyar wucewar ruwa wanda hakan ya kawo ambaliyar ruwa
Yace wajan Bayar da kwangilar Titin ma son rai aka yi aka baiwa wasu ‘yan kasar Lebanon aikin maimakon yanda aka saba bisa al’ada kowane kamfani ya gabatar da bukatarsa a duba wanda yafi cancanta.