Wani bidiyon Tauraruwar yanar gizo, Rahama Saidu ya bayyana inda aka ga ana maga zane a kirjinta wanda aka fi sani da tattoo.
Bidiyon dai ya yadu sosai inda da yawa suka rika mata fatan shiriya.
Kalli Bidiyon anan
Saidai Rahama Saidu da kanta ko kuma wata kafa bata tabbatar da sahihancin wannan bidiyon ba.
Da yawa da suka bayyana ra’yinsu akan Bidiyon sun yi mata addu’a da kuma neman tsari.
A baya dai Rahama Saidu ta shahara ne bayan da aka dakatar da ita a makarantarsu saboda bidiyo a Tiktok, sannan kuma ta zo ta kara samun suna sosai bayan da ta yi wani bidiyo na tallar kayan da take sayarwa a shagonta.