Saturday, July 20
Shadow

Bishiyar kwakwar manja:Surrukan dake tattare da Kwakwar manja ga lafiyar dan adam wajan rage hadarin kamuwa da cutar Daji da sauransu

Manja ya samo asali ne daga bishiyar kwakwa mai suna “oil palm trees “.

Yana Kunshe da sinadarai kamar haka :

– carotene

– antioxidants

– vitamin E.

Kwakwa dai kamar yadda aka sani wata diyar itace ce mai matukar amfani ga rayuwar bil’adama, kamar yadda masana a fannin kiwon lafiya suka bayyana. Kwakwa na daya daga cikin ‘ya’yan itace mai matukar amfani, saboda da irin sinadarin da Allah Ubangiji ya zuba cikin ta.

Kwakwa na dauke da ruwa cikin ta kana har ila yau ana bare jikin kwakwa sannan a ci. Kwakwa ya rabu kashi biyu, akwai kwakwar manja kana akwai kwakwa wace bata dauke da manja. Dukkanin nau’oin kwakwa dai na dauke da sinadarai da suke da matukar amfani ga rayuwar bil’adama kamar yadda masana suka bayyana.

Karanta Wannan  Abubuwan dake sa rama

WANNAN SINADARAI NA MANJA SUNA INGANTA LAFIYA TAHANYOYI KAMAR HAKA :

1)Ciwon daji

2) Cututtukan kwakwalwa

3) Cutukan idanu

4) Cutar hawan jini

5) Cutukan zuciya

6) Zazzabin cizon sauro

7) Rage taiba da nauyin jiki

Har ila yau masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana kwakwa da cewa yana kara lafiya da walwallan jiki ga bil’adama.

Saboda sinadarin “insulin” dake cikin kwakwa, masana sun bayyana kwakwa da yana rage barazanar kamuwa ko radadin cutar kansa (cancer) a jikin bil’adama.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Karanta Wannan  Kalli Hoto: Sabuwar cuta dake yaduwa ta hanyar Jima'i ta bayyana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *