
Wata Budurwa a jihar Delta me suna Brenda ta mutu bayan da ta kaiwa Saurayinta Ziyara.
Budurwar ta hadu da saurayin me suna Emmypounds ne a kafar Tiktok inda kuma ya gayyaceta zuwa dakinsa kuma ta amince.
Saidai tun bayan data ziyarceshi ba’a kara jin duriyarta ba, dan hakane wata kawarta dake da bayanan shiga shafinta na Tiktok ta shiga ta duba taga inda tace.
Ko da aka tambayi saurayin, yace ta kwanta rashin Lafiyane aka kaita Asibiti, saidai an gano ashe karyane mutuwa ta yi.