
Wata daliba dake ajin karshe na jam’ar Jihar Ekiti, EKSU me suna Helen Kayode ta yi karyar an yi garkuwa da ita amma ashe dakin saurayinta ta tafi suka sha soyayya.
Ta aikawa kanwarta da sakon cewa, ta shiga motar da ba ta gane mata ba inda daga baya tace an kaita wani kango ana tsare da ita.
Sakon nata ya watsu sosai a kafafen sada zumunta sannan hankalin mutanen Iworoko-Ekiti da Ado-Ekiti ya tashi sosai inda daga canne ta fito.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Sunday Abutu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun kama dalibar. Kuma ta amsa laifin data aikata na aika sakon garkuwa da ita amma na karya.
Hukumar ‘yansandan sun yi gargadin cewa kada a sake samun wanda yayi hakan in ba haka ba mutum zai fuskanci hukunci