Monday, July 20
Shadow

Tabbas na bayar umarnin a ciro min kàn Wike sannan a kàshè Tinubu inda har nasa ladar Naira Miliyan 100 ga wanda yayi hakan>>Nnamdi Kanu

Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB dake son lafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya aminta cewa ya sa a kashe masa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ta hanyar ciro kansa.

Sannan kuma yasa a kashe shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kona kadarorinsa, inda har ya saka ladar Naira Miliyan 100 ga duk wanda yayi hakan.

Wani shaida ne ya bayyana hakan a kotu inda yace Kani ya fadi hakanne a gidan Rediyon da ya bude.

An kuma saurari maganar da Kanu yayi wadda aka nada a cikin Kotun inda aka jishi ana cewa, a kashe Wike saboda bai cancanci rayiwa ba sannan a kashe Tinubu a kona kadarorinsa sannan a kashe jami’an tsaro.

Karanta Wannan  Duk da Hukumar Hisbah ta Kano tace ta je gidan yarin Goron Dutse ta ga ba gaskiya a zargin Luwadi da ake da yara, Saidai da yawa sun ce basu yadda da binciken na Hisbah ba, ciki kuwa hadda tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *