
Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai kama kowa ba kuma bai sa a kama kowa ba har yayi mulkinsa ya gama.
Ya bayyana hakane a martanin da yakewa Dawisu, Watau Salihu Tanko Yakasai da yace Buhari ya kamashi.
Bashir yace idan dai Dawisu zai ce an kamashi a zamanin Mulkin Buhari zai yadda amma maganar cewa Buhari yasa an kamashi ba gaskiya bane.