
Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, sun gaji mafi munin yanayin Gwamnati daga wajan Gwamnatin Buhari.
Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Benue bayan munanan hare-haren da aka kai jihar da suka yi sanadiyyar kashe mutane sama da 50.
Ya bayyana cewa, suna kokarin ganin an kawo karshen lamarin matsalar tsaro a jihar Benue kuma suna jajantawa Al’ummar da lamarin ya shafa.