Monday, March 30
Shadow

Duk Labarai

Wata Sabuwa: Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin yace sun gano hanyar da mutum zai iya rayuwar har abada ba mutuwa

Wata Sabuwa: Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin yace sun gano hanyar da mutum zai iya rayuwar har abada ba mutuwa

Duk Labarai
A yayin da kasar China ke bikin ranar samun 'yancinta ko kafuwa, shuwagabannin kasashen Korea ta Arewa da Rasha sun halarci taron. A yayin ganawarsu, an ji Shugaban China, Xi Jingping yana gayawa Putin cewa kamin yanzu ba'a cika samun mutane na kaiwa shekaru 70 ba a Duniya. Yace amma yanzu dan shekaru 70 ma za'a iya kiransa da jariri. Putin yace masa da fasahar Biotech, za'a iya canjawa mutum duk wata gaba ta jikinsa data tsufa ko ta lalace wanda hakan zai iya baiwa mutane yin rayuwa ta har abada. Shugaba Xi na China ya kara da cewa, akwai hasashen mutane zasu iya kaiwa shekaru 150 a Duniya kamin su mutu. https://twitter.com/GlobeEyeNews/status/1963248837667311795?t=atgsP8EMe7KJuUqEL9fyww&s=19
Kalli Bidiyo: Wata Mata ta bani Labarin cewa mijinta baya iya kwanciyar Aùrè da ita sai ya kawo wata cikin dakin yana kallonta tsyrara sannan zai iya biyan bukatarsa>>Inji Hajiya Bilkisu Hussaini

Shahararriyar me sayar da kayan mata, Hajiya Bilkisu Hussaini ta bayar da labarin yanda wata mata ta ce mata mijinta baya iya biyan bukata da ita sai ya kai wata mata dakinsu na aure yana kallonta tsirara sannan. Tace matar ta gaya mata cewa wani lokacin ma 'yar aiki yake sawa ta zo dakin ya rika kallonta kamin ya biya bukatarsa. Hajiya Bilkisu tace matar tace bata da wani katabus akan 'yan aikinta duk sun rainata. https://www.tiktok.com/@qissbeauty_world/video/7538704041610661176?_t=ZS-8zQAqoVJ9qj&_r=1
Bana cikin hadakar Adawa ta ADC, ba za’a hada baki dani a kayar da Tinubu zabe ba a 2027>>Inji Tsohon Minista, Hadi Sirika da EFCC ke bincikensa shi da diyarsa da mijin diyar bisa zargin almundahanar makudan kudade

Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya bayyana cewa, ba za'a hada baki dashi a kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe ba a 2027. Hadi Sirika yace baya cikin hadakar jam'iyyar 'yan Adawa ta ADC kuma baya shirin shiga. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin din Channels TV Da aka tambayeshi me ya kaishi fadar shugaban kasa, sai yace sun jene dan yiwa shugaban kasar ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Yace me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tambayeshi wai ya ji ance ya shiga jam'iyyar ADC ta hadakar 'yan Adawa inda yace masa ba gaskiya bane.
Kalli Hotuna da Bidiyo: ‘Yar Arewa, A’isha Abubakar na shan suka saboda kalar kayan data saka a wajan gasar Sarauniyar kyau ta Najeriya data shiga

Kalli Hotuna da Bidiyo: ‘Yar Arewa, A’isha Abubakar na shan suka saboda kalar kayan data saka a wajan gasar Sarauniyar kyau ta Najeriya data shiga

Duk Labarai
A'isha Abubakar wadda ta fito daga jihar Nasarawa ta shiga gasar Sarauniyar kyau ta Najeriya. Saidai abinda yafi daukar hankali game da ita shine shigarta inda ake ganin ta da kaya masu nuna surar jiki wadanda basu dace da addini da al'adar Mutanen Arewa ba. https://www.tiktok.com/@black..melaniin/video/7544462046876716296?_t=ZS-8zQ47B4cj3o&_r=1 Da yawa dai sun soke ta game da hakan inda a wasu lokutan takan mayar da martani. Saidai an yi an gama gasar kuma wadda ta fito daga jihar Anambra ce ta lashe gasar. https://www.tiktok.com/@mobilescreens_ng/video/7544487284712754452?_t=ZS-8zQ4LgwkK6D&_r=1 Hakan yasa da yawa suke wa A'isha Allah kara da fadar cewa, duk da nuna tsiraicin da ta yi amma gashinan bata ci gasar ba. https://www.tiktok.com/@black..melanii...
Sirika ya musanta zargin cewa shirin samar da ‘Nigeria Air’ na bogi ne

Sirika ya musanta zargin cewa shirin samar da ‘Nigeria Air’ na bogi ne

Duk Labarai
Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika, ya musanta zargin cewa aikin samar da kamfanin jirgin saman Najeriya na 'Nigeria Air' da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ta ƙaddamar a zamaninta na bogi ne. Sirika, wanda ya rike mukamin minista sau biyu, ya bayyana hakan ne ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata inda ya ce an bi dukkan ƙa’idoji. Ya ƙara da cewa aikin samar da jirgin saman haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da masu zaman kansu, ƙarƙashin kulawar hukumar tafiyar da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu. Tsohon ministan ya musanta batun cewa ya kashe naira biliyan 100 wajen aikin inda ya ce jimillar kuɗin da aka yi kasafi domin aikin samar da kamfanin sufurin shi ne naira biliyan 5 inda aka saki naira biliyan 3 kuma ya b...
Gwamnatin Najeriya ta bayar da hutun Maulidi

Gwamnatin Najeriya ta bayar da hutun Maulidi

Duk Labarai
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana Juma'a 5 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi na tunawa da ranar haihuwar annabi Muhammad (S.A.W). Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta fitar ranar Laraba, wadda ta samu sa hannun babbar sakatariya a ma'ikatar, Magdalene Ajani. Miliyoyin al'ummar Musulmi ne ke bukukuwan Maulidi a Najeriya da kuma faɗin duniya a duk irin wannan lokaci, kowace shekara. Sanarwar da gwamnatin Najeriyar ta fitar ta buƙaci al'ummar ƙasar su yi amfani da lokacin wajen yin addu'o'in samun zaman lafiya a ƙasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro.
APC ce silar matsalar tsaro a Najeriya ita ta kawo matsalar dan ta kawar da Jonathan daga kan mulki>>Inji Datti Baba Ahmad

APC ce silar matsalar tsaro a Najeriya ita ta kawo matsalar dan ta kawar da Jonathan daga kan mulki>>Inji Datti Baba Ahmad

Duk Labarai
Datti Baba Ahmad wanda dan takarar mataimakin shugaban kasa ne a jam'iyyar Labour party a shekarar 2023 ya bayyana cewa, jam'iyyar APC ce ta kawo matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Yace APC ce ta kawo matsalar tsaro a kokarin kawar da gwamnatin Tsohon shugaban kasa Jonathan. Yace wannan martanine maganar da El-Rufai yayi kan matsalar tsaro.
Wata Sabuwa: Gwamnatin tarayya ta cire Tallafin CNG wanda a baya ta kawo tace shine zai maye man fetur ta fara bayar da tallafi a kanshi, Kuma har farashin ya tashi sosai

Wata Sabuwa: Gwamnatin tarayya ta cire Tallafin CNG wanda a baya ta kawo tace shine zai maye man fetur ta fara bayar da tallafi a kanshi, Kuma har farashin ya tashi sosai

Duk Labarai
Rahotanni sun tabbatar da cewa farashin CNG wanda Gwamnatin Najeriyar ta kawo bayan cire tallafin man fetur tace shine zai maye man fetur ta kuma bayar da tallafi akansa farashinsa yayi sauki sosai a yanzu ta cire masa tallafi kuma har farashinsa ya nunka. Rahoton da muke samu daga Punchng ya tabbatar mana da cewa, farashin na CNG ya tashi ya kai Naira 450, ga manyan motoci inda kananan motoci kuma ke sha akan farashin 380. Shugaban shirin na CNG, Michael Oluwagbemi yaki daukar waya dan yin bayanin dalilin cire tallafin. Saidai wani na kusa dashi da bai so a kira sunansa ya tabbatarwa da Punchng chire tallafin inda yace yanzu tashoshin CNG din na sayar da shi a farashi mabanbanta amma ya danganta da kalar motar da mutum ya je sayen CNG din da ita.
Ashe matsalar ba ta Rashin Ilimi bace: Wallahi Nasan Yaran dan damisa guda 4 duk mahaddata Qur’anine>>Inji Rabeeat

Ashe matsalar ba ta Rashin Ilimi bace: Wallahi Nasan Yaran dan damisa guda 4 duk mahaddata Qur’anine>>Inji Rabeeat

Duk Labarai
Bayan rasuwar kasurgumin dan daba dake kaduna, Habu Dan Damusa, an rika samun mutane wasu na Allah wadai wasu kuma na jinjinawa gareshi. Wata me suna Rabeeat data bayyana cewa ta sanshi tace matsalar ba ta rashin Ilimi bace Tace yaransa guda 4 duk mahaddata Qur'anine inda tace PA dinsa ma mahaddacin Qur'anine. Tace Addu'a ce kawai mafita inda tace me unguwarsu da ya rika tsine musu shima yaransa duk sun shiga daba. Tace dan haka ida mutum ya musu Addu'a, kamar yawa 'ya'yansa ne.
Kalli Bidiyon: Sheikh Bin Usman ya mayarwa da Sheikh Maqari martani inda yace du wanda yace wanda baya Maulidi ba musulmi bane to yace sahabbai ba musulmai bane saboda basu yi Maulidi ba

Kalli Bidiyon: Sheikh Bin Usman ya mayarwa da Sheikh Maqari martani inda yace du wanda yace wanda baya Maulidi ba musulmi bane to yace sahabbai ba musulmai bane saboda basu yi Maulidi ba

Duk Labarai
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Bin Usman ya mayarwa da Sheikh Maqari martani kan ikirarin Sheikh Maqari na cewa, duk wanda ba ya maulidi ba musulmi bane. Sheikh bin Usman yace duk wanda yace wanda baya Maulidi ba musulmi bane to yace sahabbai ba musulmai bane dan basu yi maulidi ba. https://www.tiktok.com/@_sadiq_07/video/7544050335359307026?_t=ZS-8zP3p6xOleb&_r=1