Sunday, December 14
Shadow

Duk Labarai

Jihar Kebbi na son saka dokar kisa ga masu baiwa masu garkuwa da mutane bayanan sirri

Jihar Kebbi na son saka dokar kisa ga masu baiwa masu garkuwa da mutane bayanan sirri

Duk Labarai
Jihar Kebbi na son saka dokar kisa ga masu baiwa masu garkuwa da mutane bayanan sirri. Gwamnan jihar, Comrade Nasiru Idris yace zasu saka dokar kisa ko kuma daurin rai da rai ga masu baiwa masu garkuwa da mutanen bayanan sirri. Ya bayyana hakane a yayin da ya kai ziyara kauyukan Tadurga da Zuru da Kyebu inda ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda 'yan Bindiga suka kashe. Kauyukan na kananan hukumomin Danko/Wasagu dake jihar kuma kwanannan aka kai hare-hare wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 30 da kuma sace shanu da yawa. Gwamnan ya bayyana cewa, zasu dauki matsalar tsaro da matukar muhimmanci a jihar.
SANÀRWAŔ GAGGÀWA: Wannan Mutumin Yana Mai Kira Ga ‘Ýàn Arewa Cewa Da Su Guji Bin Hànyar Makurdì A Yanzù Domiñ ‘Ýàn Kabìlar ȚV Suña Taŕe Hañya Da Sunàn Daukàr Fansà Sakamakoñ Wani Harìn Da Suke Zaŕgìn Fuĺàni Makiýaýa Sun Kài Musù

SANÀRWAŔ GAGGÀWA: Wannan Mutumin Yana Mai Kira Ga ‘Ýàn Arewa Cewa Da Su Guji Bin Hànyar Makurdì A Yanzù Domiñ ‘Ýàn Kabìlar ȚV Suña Taŕe Hañya Da Sunàn Daukàr Fansà Sakamakoñ Wani Harìn Da Suke Zaŕgìn Fuĺàni Makiýaýa Sun Kài Musù

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} SANÀRWAŔ GAGGÀWA: Wannan Mutumin Yana Mai Kira Ga 'Ýàn Arewa Cewa Da Su Guji Bin Hànyar Makurdì A Yanzù Domiñ 'Ýàn Kabìlar ȚV Suña Taŕe Hañya Da Sunàn Daukàr Fansà Sakamakoñ Wani Harìn Da Suke Zaŕgìn Fuĺàni Makiýaýa Sun Kài Musù Ya ce su ma da kyaŕ sukà shà. Jama'a akwai bukatar a yada (sharing) domin amfanar matafiya masu bin hanyaŕ.
Kalli Bidiyon bikin Malika da Abdul M. Shareef da ya dauki hankula

Kalli Bidiyon bikin Malika da Abdul M. Shareef da ya dauki hankula

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Malika kenan ko ace Amarya a wadannan Bidiyon inda ta dauki hankula sosai bayan da aka ganta ta sha kwalliya irin ta amare. Malika wadda abokin aikinta, Abdul M. Shareef zai aura an ganta a Bidiyon tare da kawayenta suna taka rawa. https://www.tiktok.com/@nayarhhh/video/7519588298487057669?_t=ZM-8xUhraJAZ1R&_r=1 https://www.tiktok.com/@nayarhhh/video/7519644509362244870?_t=ZM-8xUiBy8QaZC&_r=1 Da yawa dai sun ce ta yi kyau.
Tinubu siyasa ya iya, bai iya Mulki ba>>Inji Dan takarar shugaban kasa na SDP, Adewole Adebayo

Tinubu siyasa ya iya, bai iya Mulki ba>>Inji Dan takarar shugaban kasa na SDP, Adewole Adebayo

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo ya bayyana cewa, shuaban kasa, Bola Ahmad Tinubu siyasa ya iya amma bai iya mulki ba. Ya bayyana hakane a hirar da kafar Vanguard ta yi dashi inda yace Tinubu ya san 'yan siyasa kuma yasan me suke da bukata kuma yana musu. Yace amma ya kasa mayar da hankali dan fahimtar abinda mutane ke bukata dan su ma ya musu. Yace Mutane abinda suke bukata shine tsaro da kawar da talauci. Yace abinda ya kamata Tinubu ya fahimta shine ba sai ya tara 'yan siyasa a jikinsa ba, idan ya biyawa Talakawa bukatunsu zai iya cin zabe.
Rikici ya kunno kai a jam’iyyar su El-Rufai ta SDP an dakatar da shugaban jam’iyyar saboda zargin satar kudin jam’iyyar

Rikici ya kunno kai a jam’iyyar su El-Rufai ta SDP an dakatar da shugaban jam’iyyar saboda zargin satar kudin jam’iyyar

Duk Labarai
Jam'iyyar SDP ta sanar da dakatar da shugabanta, Shehu Gabam bisa zargin aikata ba daidai ba da wasu kudaden jam'iyyar. Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Araba Aiyenigba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata inda yace bayan shugaban SDP din, an kuma dakatar da me binciken gudanar kudi na jam'iyyar, Nnadi Clarkson, da kuma shugaban matasa na jam'iyyar, Chukwuma Uchechukwu. Yace kudaden da ake zarginsu da cinyewa sun hada da na siyen fom din takara a zaben 2023 kuma kudaden Miliyoyin Naira ne. Yace an saka mataimakin shugaban jam'iyyar, Sadiq Abubaka a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na riko. Yace kuma sun sanar da hukumar zabe da dukkan hukumomin da suka kamata game da dakatarwar.
Darajar Naira ta Farfado a kasuwar canji

Darajar Naira ta Farfado a kasuwar canji

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa darajar Naira ta dan farfado a kasuwar Chanji inda aka rika sayen dala akan Naira 1595 ranar Talata. Idan aka kwatanta da farashin dalar na naira 1600 da aka rika saye a ranar Litinin, za'a iya cewa darajar Nairar ta karu da Naira 5. Saidai farashin nairar a kasuwar Gwamnati shine ana sayen dala akan Naira 1550.
A zaben 2027 ba zamu saki baki a mana abinda aka ga dama ba>>Atiku Abubakar ya bayyana shirin cin zabe na musamman da yake yi

A zaben 2027 ba zamu saki baki a mana abinda aka ga dama ba>>Atiku Abubakar ya bayyana shirin cin zabe na musamman da yake yi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2027, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa zaben 2027 ba zai zama kamar sauran zabukan da aka yi a baya ba. Yace 'yan adawa na hadaka ta musamman dan ganin sun yi nasara akan gwamnati me ci saboda tsare-tsaren gwamnatin basu kawowa kasar ci gaba ba. Ya bayyana hakane a Abuja ranar Talata a yayin ziyarar da wasu 'yan masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood suka kai masa. Kungiyar tace tana tare da Atiku a zabe me zuwa. Wani dan siyasa daga jihar Zamfara, Dr. Aslam Aliyu ne yawa kungiyar jagora zuwa wajan Atiku.
‘Yan sanda basu kama mutane saboda zagin ‘yan siyasa, har ni ku zaga babu wanda zai kamaku>>Inji Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun

‘Yan sanda basu kama mutane saboda zagin ‘yan siyasa, har ni ku zaga babu wanda zai kamaku>>Inji Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa, 'yansanda basa kama mutum dan kawai ya zagi ko sukar dan siyasa. Yace koshi ana zaginshi a kafafen sada zumunta amma hakan baya sawa a kama mutane. Ya bayyana hakane ranar Talata a wajan wani taron da aka gudanar a Abuja inda yace amma inda za'a iya kama mutum shine idan ya wallafa labaran karya. Yace ko da ba akan dan siyasa ba idan mutum ya wallafa labaran karya za'a iya hukuntashi.
Gaf nake da barin jam’iyyar APC saboda alamu na nuna ba lallai Tinubu ya kai labari ba duk da gwamnonin dake tururuwar komawa jam’iyyar APC>>Sanata Ali Ndume

Gaf nake da barin jam’iyyar APC saboda alamu na nuna ba lallai Tinubu ya kai labari ba duk da gwamnonin dake tururuwar komawa jam’iyyar APC>>Sanata Ali Ndume

Duk Labarai
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya bayyana cewa, gaf yake da barin jam'iyyar APC saboda ba lallai jam'iyyar ta kai labari ba a zaben 2027. Ndume a wata hira da aka yi dashi a Arise TV yace a baya yayi imanin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai iya gayara matsalolin Najeriya amma daga baya abubuwa suka canja. Ya bayyana cewa, maganar gaskiya shi tuni ma ya fara halartat tarukan hadakar 'yan Adawa dan kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027. Yace amma har yanzu bai yankewa shugaban kasar tsammanin yin gyara ba amma idan aka ci gaba a haka, shi zai fice daga jam'iyyar.