Monday, December 15
Shadow

Duk Labarai

Yawan ‘yan majalisar APC ya karu a majalisar tarayya bayan canja sheka da ‘yan PDP da Labour  party da NNPP suka yi ta yi

Yawan ‘yan majalisar APC ya karu a majalisar tarayya bayan canja sheka da ‘yan PDP da Labour party da NNPP suka yi ta yi

Duk Labarai
Yawan 'yan majalisar Jam'iyyar APC a majalisar tarayya ya karu bayan da 'yan jam'iyyar Hamayya suka rika canja sheka kamar farin dango. A yanzu yawan 'yan majalisar dattijai na jam'iyyar APC sun karu zuwa 68 a yayin da yawan 'yan majalisar wakilanta suka karu zuwa 207. Hakan na zuwane yayin da majalisar ta 10 ta cika shekaru 2 da kafuwa. Idan rahotannin dake cewa sanata Senator Neda Imasuen daga jihar Edo dan jam'iyyar Labour party zai canja sheka zuwa jam'iyyar APC suka tabbata, to yawan 'yan majalisar Dattijai na jam'iyyar zai karu zuwa 69 kenan. Hakanan yawan sanatocin APC din zasu karu idan Sanata Ahmed Wadada Aliyu daga jihar Nasarawa wanda ya bar jam'iyyar SDP ya koma jam'iyyar APC. Ana zargin jam'iyyar APC da kokarin mayar da Najeriya tsarin jam'iyya daya.
Kasar Ìràn tace idan dai Amurka na son a yi sulhu kan shirin ta na mallakar makamin kare dangi, to itace zata gindaya sharudan da za’a bi ba Amurkace zata mata katsalandan ba

Kasar Ìràn tace idan dai Amurka na son a yi sulhu kan shirin ta na mallakar makamin kare dangi, to itace zata gindaya sharudan da za’a bi ba Amurkace zata mata katsalandan ba

Duk Labarai
Kasar Iran tace bata aminta da sharudan da kasar Amurka ta gindaya mata na maganar sulhun makamin kare dangin da take son mallaka ba. Iran tace ita kasa ce me cin gashin kanta dan haka ba zata saurari Amurka ta bata sharadi akan yanda zata gudanar da kasarta ba ko makamin kare danginta ba. Iran tace idan dai ana son tattaunawar ta ci gaba, to itace zata gindaya sharudan da za'a bi wajan ci gaba da tattaunawar.
Kiris ya hana in daina karatun saboda takurar malamai>>Matar Tsohon Shugaban kasa, Patience Jonathan bayan ta kammala karatun Digiri na 3

Kiris ya hana in daina karatun saboda takurar malamai>>Matar Tsohon Shugaban kasa, Patience Jonathan bayan ta kammala karatun Digiri na 3

Duk Labarai
Matar tsohon Shugaban kasa, Patience Jonathan bayan ta kammala karatun Digiri na 3 watau PhD ta bayyana irin wahalar da ta sha. Ta bayyana hakane a wajan taron cocin Streams of Joy International Church. Tace a lokacin da ta je sayen fom din fara karatun ta rika kokwanton ko zata iya, shin me ma zata yi da wannan karatun tunda da ta zama har matar shugaban kasa? Tace amma ta karfafa kanta inda tace idan 'ya'yanta zasu iya to itama zata iya. Tace malamai idan ta kai musu aikinta sai su rika ce mata taje ta gyara guri kaza da kaza, tace hakan yana sa ta tambayi cewa shin wadannan basu san cewa ta tsufa ba? Tace a haka dai Allah ya taimaketa ta kammala karatun.
Tunubu yafi Atiku da Peter Obi wayau>>Inji Wani Me fada aji a yankin Yarbawa

Tunubu yafi Atiku da Peter Obi wayau>>Inji Wani Me fada aji a yankin Yarbawa

Duk Labarai
Wani me fana aji a yankin yarbawa wanda kuma dan PDP ne ne suna Segun Sowunmi ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yafi Atiku Abubakar da Peter Obi wayau. Segun Sowunmi tsohon me magana da yawun Atiku ne wanda yace haduwarsa da Tinubu ba tana nufin ya ci Amanar Atiku bane. Yace a matsayinsa na mutum me hankali yana da 'yancin yin abinda yake so. Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV duk da yake cewa a baya ya soki gwamnatin Tinubu sosai.
Kalli Bidiyo: An kama Dan Banga, da suka je kama me Gàrkùwà da mutane suka iske baya nan sai suka yiwa matarsa Fyàdè

Kalli Bidiyo: An kama Dan Banga, da suka je kama me Gàrkùwà da mutane suka iske baya nan sai suka yiwa matarsa Fyàdè

Duk Labarai
Wani dan banga da aka kama ya dauki hankula a kafafen sada zumunta saboda laifin da ya aikata. Sun je kama me garkuwa da mutanene sai suka tarar da baya gida amma sai matarsa https://twitter.com/Dongarrus1/status/1932060506275061812?t=hIo8JSRAwGBbjGq1El7PyQ&s=19 Anan suka nemi yin lalata da ita kuma ta basu hadin kai, saidai daga baya an kamasu.
Tinubu ne ke daukar nauyin rikicin dake faruwa a jam’iyyar mu ta Labour party>>Peter Obi

Tinubu ne ke daukar nauyin rikicin dake faruwa a jam’iyyar mu ta Labour party>>Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ke da alhakin rikicin dake faruwa a cikin jam'iyyar su. Obi ya bayyana hakane a yayin da ake masa tambayoyi a gidan Talabijin na Arise TV inda yace yana da tabbacin Gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyin rikicin dake faruwa a jam'iyyar. Ya bayyana cewa, suna son yada rikici a cikin jam'iyyar ta Labour Party.
Jigo a Jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi yace a shirye yake ya koma APC duk da a baya ya soki jam’iyyar

Jigo a Jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi yace a shirye yake ya koma APC duk da a baya ya soki jam’iyyar

Duk Labarai
Jigo a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi ya bayyana cewa, a Shirye yake ya koma jam'iyyar APC duk da a baya ya soki jam'iyyar da salon mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Yace lallai a baya ya soki Gwamnatin Tinubu amma a yanzu idan dai ya samu dama, zai iya komawa jam'iyyar APC. Yace kuma a shirye yake dan yin aiki tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu din domin ko da a baya dama yayi aiki tare dashi.
Ji yanda Bòm ya kàshè masu yawon murnar sallah a Sakkwato

Ji yanda Bòm ya kàshè masu yawon murnar sallah a Sakkwato

Duk Labarai
Kimanin mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya bayan tarwatsewar wani abun fashewa da ake zargi mayaƙan Lakurawa sun dasa a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato. Aminiya ta ruwaito cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su da ke kan babura na hanyarsu ta dawowa daga yawon bikin sallah a ƙauyen Gwabro. Bayanai sun ce an dasa abun fashewar ne a ƙarƙashin wata itaciya da ke zaman wurin hutawar dakarun sojoji a lokacin da suka fito sintiri a yankin. Majiyiyo sun ce mutum shida sun mutu nan take yayin da ɗaya daga cikin wasu mata biyu yara da suka jikkata ta rasu washegari. Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Tangaza, Alhaji Ghazzali Rakah ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa waɗanda abin ya shafa mazauna ƙauyen Zurmuku ne. Wannan dai ba shi na farau ba, domin kuwa a watan...
Ji bayani Dalla-Dalla: DA KYAR JAMI’AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA

Ji bayani Dalla-Dalla: DA KYAR JAMI’AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA

Duk Labarai
DA KYAR JAMI'AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA. Rahotanni daga Jihar Kano sun bayyana bayyana cewar sai dai aka hada da jami'an tsaro aka ceci Dan wasan barkwanco Ali Art-work Wanda aka fi sani da Madagwal. Madagwal ya fada komar Yan Kwankwasiyya ne jiya Lahadi lokacin daya sake zuwa karbar darikar Kwankwasiyyar, a hannun Ubanta Injiniya Rabiu Musa, a wani taro da suka gudanar na bikin Sallah a Jihar. Kafin Yanzu bayan ficewar sa a shekararun baya Madagwal ya koma suka da jefa kalaman batanci ga Rabiu Musa Kwankwaso da sauran Magoya bayan sa. Haka Kuma ya sha chachchakar salon Mulkin Abba Kabir Yusuf, tare da bukatar cewar Kwankwaso ya yiwa Gwamnatin Jihar Kano kakagida shi yasa baa tabuka abun a zo a gani. Wannan ya Saka ...