Ji dabarun da Shugaba Tinubu ke amfani dasu wajan jawo hankalin ‘yan Adawa zuwa APC
Kusan za a iya cewa da wuya gari ya waye a Najeriya ba tare da ƴan siyasa daga jam'iyyun hamayya sun sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki ba, walau dai a matakin tarayya ko kuma jihohi da ƙananan hukumomi.
Sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC da ya fi bai wa ƴan Najeriya mamaki a baya-bayan nan shi ne na ]tsohon ɗantakarar mataimakin shugaban ƙasa na babbar jam'iyya mai hamayya ta PDP, kuma tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Efeanyi Okowa tare da gwamnan jihar mai ci, Sheriff Oborevwori.
Bugu da ƙari, ko a wannan makon ma sai da jam'iyyar mai mulki ta karɓi sabbin masu sauya sheƙa daga jam'iyyar hamayya ta PDP daga jihar Kebbi, inda duka ƴan majalisar dattawan jihar suka koma APC.
Wannan ya janyo ƴan Najeriya ke neman sanin irin dubarun da jam'iyya mai mulkin ke bi wajen...








