Na yafe wa waɗanda su ka mini ƙage da sharri da ƙazafi – Amarya Aisha Humaira
Aisha Humaira, amaryar kuma abokiyar aikin mawaki Dauda Kahutu Rarara ta magantu a karon farko bayan auren su, wanda aka daura a Maiduguri a ranar Juma'a.
A wani faifen bidiyo da ya karade kafafen sadarwa, an gano Aisha Humaira sanye da hijabi tana kira ga waɗanda ke fadar maganganu na ƙage akan alaƙar ta da Rarara da su dena kuma ta yafe musu.
"Ina masharranta, ina munafukai, ina masu shedar zir, ko kuma wani ya ji labari ha je ya dorar? Ina masu zama su ce wance ta yi kaza, wane ya yi kaza, an yi kaza, an yi kaza kuma bayan duk basu gani ba ba su ji ba.
"Ina wadanda su ka zage ni ban sani ba, ina waɗanda su ka zage ni na sani? Ina magulmata masu kaiwa da kawowa, masu cewa Aisha Humaira ta yi kaza, ta yi kaza?
"Duk wanda ya zage ni a bayan ido na da wanda ya zage ni d gaban wa...








