YANZU-YANZU: Real Madrid Ta Bude Sabuwar Shekarar 2025 Da Yin Nasara, Inda Ta Yi Wa Valancia Ci 2-1 A Mintin Karshe
Nasarar ta Madrid na zuwa ne duk da cewa an baiwa dan wasanta guda daya jan kati, wato Vinicius Junior.
Me za ku ce?
Makaho Ne, Amma Ya Fi Wasu Da Dama Gani Ta Zuci
Wannan shine makahon da ya yi takarar izu 60 da tafseeri, tajweedi, shadibiyya da kuma rubutu. Kuma cikin ikon Allah danja daya ya tashi da shi.
Wannan tabbas baiwa ce babba daga Allah.
Daga Khalid Yusuf Sambo
Tsohon hadimin Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari me suna Babafemi Ojudu da yayi aikin bada shawara akan harkar siyasa a ofishin tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Buhari bai so Osinbajo ko Tinubu su zama shugaban Najeriya ba.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a wani gidan rediyo na yanar gizo me suna Edmund Obilo’s State Affairs.
Ya kuma ce zagayen neman delegates kadai bai isa ba su ci zabe inda yace kamata yayi ace shugaba Buhari ya baiwa hadimansa baki kan su taimakaw Osinbajo amma yaki.
Yace koda Tinubu ma yawa Buharin wayaune shiyasa ya samu nasara.
Kungiyar kamfanonin sadarwa sun nemi gwamnati ta basu dama su nunka kudin kati dana data.
Wakilin kamfanin MTN, Karl Toriola ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise TV yayi dashi.
Saidai ya bayyana cewa da wuya, musamman saboda halin matsi da mutane ke ciki Gwamnati ta amince da bukatar tasu.
Yace amma karin ya zama dolene saboda la'akari da kudin da suke kashewa wajan yin aiki da hauhawar farashin kayan masarufi da kuma karuwar yawan mutanen dake amfani da waya.
Dogarin shugaban kasar Ghana, Colonel Isaac Amponsah ya yanke jiki ya fadi a yayin da shugaban kasar kewa majalisar kasar jawabi.
Lamarin ya farune ranar January 3, 2025 inda nan da nan mutane suka kaiwa dogarin dauki, bayan bashi kulawar gaggawa, an kuma garzaya dashi zuwa Asibiti.
Shugaban kasar Ghanan, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya dakatar da jawabin nasa inda ya juya dan tabbatar da hadimin nasa ya samu kulawa, kamin daga baya ya juya ya ci gaba da yin jawabin.
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bayyana cewa suna kan aikin gyaran matatar man Kaduna data Fatakwal.
Yace za'a yiwa matatan man fetur din aikin da zasu sama aun zo daidai da takwarorinsu na sauran kasashen Duniya ne.
Ya kuma bayyana cewa matatun man fetur na Fatakwal da Warri da aka kammala an kammalasu ne bayan yi musu gyaran da zasu yi gogayya da sauran na kasashen Duniya.
Shugaban bangaren yada labarai na kamfanin ne ya bayyana hakan.
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, ana tsammanin za'a dauke wutar lantarki a Abujan na tsawon makonni 2.
Kamfanin rarraba wutar na Abuja, AEDC ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar inda yace za'a fara samun matsalar ne daga ranar Litinin, 6 ga watan Janairu zuwa 21 ga watan.
Kamfanin yace hakan zai farune dalilin wani gyara da zasu yi.
Guraren da matsalar zata shafa sun hada da Lugbe, Airport Road, Kapwa, NNPC, Games Village, National Stadium, Eye Clinic, Indoor Complex, Christ Embassy Church, American International School, Spring Court, American Embassy Quarters, EFCC Headquarters, Coca Cola, Railway, da Federal Medical Centre (FMC), Jabi.
Sai kuma Apo, Gudu, Gbazango, Kubwa, Bwari, Jahi, Jabi, Karu, Nyanya, Mararaba, Keffi.
A karshe kamfanin ya bayar...
Wata mata ta bayyana burinta na son yin lalata da maza 1000 a rana daya.
Tana son yin hakanne dan shiga kundin tarihi na Duniya wansa ake kira da Guinness world record.
https://www.youtube.com/watch?v=GlwuIJ7jPPY?si=srzDsdNbM_jkZLoI
Macen dake da kambun yanzu a hannunta ta yi lalata da maza 919 ne a rana daya.
Wani mutum ya kashe kansa ranar Juma'a a yankin Enyenkorin na garin Ilorin dake jihar Kwara.
Mutumin ya kashe kansa ne ta hanyar rataya a jikin Bishiya.
Wani mutum da ya shaida lamarin yace sun iske wata takarda a jikin mutumin inda ya rubuta lambar dan uwansa da matarsa a jihar Gombe.
Tuni dai 'yansanda suka isa wajan inda suka kai gawar mamacin mutuware.