Monday, June 29
Shadow

Duk Labarai

ABIN ALFAHRI: Matashi Dan Arewa Na Farko Da Ya Kammala Karatu A Fannin Magungunan Musulunci A Kasar Qatar

ABIN ALFAHRI: Matashi Dan Arewa Na Farko Da Ya Kammala Karatu A Fannin Magungunan Musulunci A Kasar Qatar

Duk Labarai
ABIN ALFAHRI: Matashi Dan Arewa Na Farko Da Ya Kammala Karatu A Fannin Magungunan Musulunci A Kasar Qatar. Dakta Muhammadu Kabiru Hassan (Dangwamna) dake Samaru Zaria ya zama mutum na farko da ya fito daga yankin Arewacin Nijeriya da ya kammala karantu a kasar Qatar National Museums Authority bangaren islamic herbal medicine curse. Daga karshe ya nemi jama'a da su yi masa addu'ada fatan alkairi, Allah Ya sa karatun da ya yi ya amfani muśùĺùñci gaba daya.
DA DUMI-DUMI: Sojoji Sun Harbe Wani DPO Na ‘Yan Sanda A Jihar Zamfara Har Lahira Kan Zargin Safarar Makamai

DA DUMI-DUMI: Sojoji Sun Harbe Wani DPO Na ‘Yan Sanda A Jihar Zamfara Har Lahira Kan Zargin Safarar Makamai

Duk Labarai
DA DUMI-DUMI: Sojoji Sun Harbe Wani DPO Na 'Yan Sanda A Jihar Zamfara Har Lahira Kan Zargin Safarar Makamai. Al'amarin dai ya faru ne a garin Ɗanmarke da ke karƙashin ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara, a ranar Larabar nan da daddare, kamar yadda wata sanarwa da rundunar ƴansandan jihar ta Zamfara ta fitar. Dpon an tsaida shi a checkpoint na dan marke da ke cikin Karama Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara ya ki tsayawa, wanda hakan yasa sojoji suka yi waya gaba domin su rufe hanya ga mota nan zuwa mai kala kaza, ga sunan zuwa. Nan da nan suka bi umurnin soji nan take sojoji su ka biyo motarsa yana zuwa ya isko an rufe hanya, bayan ya bayyana kan sa matsayin ɗan sanda ne, sai kuma ya fita daga motar zai gudu wanda hakan yasa sojojin suka bude masa wuta. Daga bisani ...
Atiku ya caccaki manufofin Tinubu kan ƙayyade shekarun shiga jami’a

Atiku ya caccaki manufofin Tinubu kan ƙayyade shekarun shiga jami’a

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga manufar ma’aikatar ilimi ta tarayya na kayyade shekarun shiga jami’o’i, inda ya bayyana hakan a matsayin wani baƙon abu da zai janyo komabaya ga harkar ilimi a Najeriya A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana manufar a matsayin "zai haifar da naƙasu ga hakar ilimi" inda ya ce hakan ya saɓa wa ƙa'idojin tsarin ƙasar ta hanyar shiga ayyukan gwamnatocin jihohi. Atiku ya yi nuni da cewa ilimi na cikin abubuwan da ke cikin ƙundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa ƙananan hukumomin ƙasar karfi wajen tafiyar da harkokinsa. Ya yi allah-wadai da matakin da gwamnati ta ɗauka na kafa manufofin ilimi ba kamar yadda doka ta tanada ba inda ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasa...
Zanga-zanga: An saki Turawan da ake zargi da hannu a ɗaga tutar Rasha a Najeriya

Zanga-zanga: An saki Turawan da ake zargi da hannu a ɗaga tutar Rasha a Najeriya

Duk Labarai
An saki ɗalibai da malamai ƴan asalin ƙasar Poland da aka kama a lokacin da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Poland ya bayyana a ranar Laraba. Mutum bakwan sun shiga hannu ne a Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, "bisa zargin su da hannu a ɗaga tutocin Rasha da ma ita kanta zanga-zangar," kamar yadda jami'an tsaron Najeriya suka bayyana. Sai dai hukumomi a ƙasar Poland sun ce waɗanda aka kama ɗin ɗalibai ne na Jami'ar Warsaw da malaminsu, waɗanda "tsautsayi ya kai su inda bai dace ba." Ministan Harkokin Wajen Poland, Radoslaw Sikorski ya ce yanzu an sako ɗaliban. "Ina tabbatar da cewa an sako mutanenmu ɗin nan, yanzu haka sun koma Kano sun ci gaba da karatunsu," kamar yadda Sikorski ya wallafa wani bidiyo a shafi X. Ya ƙara da...
‘Ya kamata a ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a Najeriya’

‘Ya kamata a ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a Najeriya’

Duk Labarai
Cibiyar tattarawa da yaɗa bayanai kan rikice-rikice (CCC) ta yi gargaɗin cewa garkuwa da mutane na ƙaruwa a Najeriya, inda ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyarv ƙasar da ta ayyana dokar ta-ɓaci domin magance matsalar. Shugaban CCC, Manjo Janar Chris Olukolade, mai ritaya, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa matsalolin za su iya ta'azzara idan ba a yi abin da ya dace ba, wanda hakan zai ƙara jefa rayuwar al'umma cikin matsala da ƙara taɓarɓarar da matsalar tsaro. Sanarwar ta ƙara da cewa garkuwa da mutane ta rikiɗe zuwa wata babbar harka ta kasuwanci, inda ƙungiyoyin ta'addanci ke amfani da lamarin domin samun kuɗin shiga. "Sace mutum da aka yi na kwana-nan shi ne sace basarake a Masarautar Sokoto, da sace ɗaliban jami'a masu karatun kiwon lafiya guda 20, waɗanda aka sako daga ...
Muna yin bakin ƙoƙarinmu kan matsalar tsaro – Gwamnatin Sokoto

Muna yin bakin ƙoƙarinmu kan matsalar tsaro – Gwamnatin Sokoto

Duk Labarai
Bayan an shafe kwanaki ana sukar yadda gwamnatin jihar Sokoto ke tafiyar da sha’anin tsaro, musamman bayan garkuwa da kuma kashe Sarkin Gobir na Gatawa, a yanzu hukumomin jihar sun bayyana cewa suna iyakar ƙoƙarinsu kan matsalar. A makon da ya gabata ne ƴan bindiga suka kashe Sarkin Gobir, Muhammad Isa Bawa, bayan yin garkuwa da shi na sama da mako uku, lamarin da ya janyo wa hukumomi kakkausar suka. Wasu dai a Najeriya na zargin hukumomi da gaza yin abin da ya kamata wajen kawar da matsalar tsaro a faɗin ƙasar. Ƴan fashin daji na kai hare-hare a jihohin arewa maso yammacin ƙasar, yayin da har yanzu ake fuskantar hare-hare nan-da-can na ƙungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas. Hukumomin Najeriya dai sun ce suna bakin ƙoƙarinsu wajen magance matsalar. Sai dai kisan da a...