Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima basa Najeriya, Saidai Fadar shugaban kasa tace Shugabancin Najeriya ba zai samu Tangarda ba
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa,Kashim Shettima basa Najeriya.
A yayin da shugaba Tinubu ya tafi kasar Ingila inda daga can ya wuce Faransa.
Shi kuwa mataimakinsa, Kashim Shettima ya tafi kasar Sweden ne.
Babban me baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya bayyana cewa hakan ba zai kawo tangarda ga shugabancin kasarnan ba.
Yace a yanzu da ake da kafafen sadarwa na Zamani duk inda shuwagabannin suke suna gudanar da ayyukansu yanda ya kamata.
Yace shugaba Tinubu ya tafi hutun sati 2 ne yayin da shi kuma Mataimakinsa,Kashim Shettima ya tafi kasar Sweden wajan gudanar wa da Najeriya aiki.