PDP Ta Sanya Ranar Da Za ta Yi Taron NEC Karo Na Biyu
PDP Ta Sanya Ranar Da Za ta Yi Taron NEC Karo Na Biyu
Jam’iyyar PDP ta bayyana ranar Alhamis 26 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa karo na biyu a shekarar 2024.
Idan za a iya tunawa, a taron farko da hukumar NEC ta gudanar a ranar 18 ga watan Afrilu,an tattauna batutuwan da suka hada da makomar mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Illiya Damagum, an daga shi zuwa taron NEC na gaba wanda aka shirya tun watan Agusta.
Kungiyar ‘yan jam’iyyar ta Arewa ta tsakiya ta ce za a zabi dan takara daga shiyyar don kammala wa’adin tsohon shugaban Jam'iyyar na kasa, Dr. Iyiorchia Ayu, wanda ya yi murabus kusan shekaru biyu cikin wa'adinsa na shekaru hudu.
Gabanin taron NEC na watan Satumba, jam’iyyar ta tsayar da ranar 27 ga wata...