Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 – NLC
Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 - NLC
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta ce gwamnonin jihohin ƙasar za su iya biyan foye da naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, idan suka rage cin hanci da rashawa da kuɗin da suka kashewa wajen gudanar da mulki a jihohinsu.
Aranar Juma'a ne dai ƙungiyar gwmanonin ta fitar da wata sanarwar da a ciki take cewa gwamnonin jihohin ƙasar 36 ba za su iya biyan naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata ba.
To sai dai a cikin martanin da ta mayar ƙungiyar ta NLC, ta yi Allah wadai da sanarwar gwamnonin.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NLC, Benson Upah,ya fitar ya ce idan gwamnaonin suka mayar da hankali babu abin da zai hana su biyan mafi ƙarancin albashin.
''Koda nawa ne mafi ƙa...