Kalolin ruwan gaban mace
Kin taba tunanin ko kalolin ruwan dake fita daga gaban mace guda nawane? A wannan rubutun,mun kawo muku cikakken bayani kan yawan kalolin ruwan dake fita daga gaban mace da kuma ma'anar kowanne.
Ga su kamar haka:
Ruwan dake fita a gaban mace abune da yawancin mata sun saba dashi, kuma yana fitane dan wanke da tsaftace gaban macen daga lokaci zuwa lokaci.
Ba abune na tashin hankali ba amma ya kamata a lura da canje-canje a kalolin ruwan da kuma yanayin jiki wanda ka iya sanyawa a gane shigar cuta.
Fitar Farin Ruwa:
Farin ruwa wanda wani lokacin yakan iya zama me yauki ko me ruwa-ruwa a gaban mace bashi da matsala.
Wani lokacin ma zaki ga ya bata miki wando, a wani lokacin ida kina jin sha'awa zaki iya jin wannan ruwa wanda yana zuwane dan saukaka yin jima'i.
Hakanan kum...