Gyaran fuska da manja
Akwai hanyoyi da yawa da ake gyaran fuska da man ja.
Ga wasu daga ciki kamar haka:
A wanke fuska dan fitar da duk wani datti, a saka tsumma a tsane fuskar.
Daga nan sai a shafa man ja, a bari ya dan jiku a fuskar sai a goge.
Hakan yana kawar da duk wani duhun fata.
Ana kuma iya diga man ja a cikin man shafawa ko man wanka da sauransu.
A wani kaulin, an ruwaito man ja na kawar da tabon kuna wanda bai yi zurfi ba sosai, sannan yana kawar da tabon kurajen fuska da yankewa wadda bata yi zurfi ba sosai.
Hakanan wani kaulin ya bayyana manja na maganin tattarewar fuska ta tsufa, fuskar mutum ba zata tattare sosai ba.