Aikin Hajji: Karin Wani Mahajjacin Daga Jihar Kebbi Ya Rasu A Makkah
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi ta sanar da rasuwar wani Mahajjacin jihar a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da kungiyar yada labarai ta Kebbi Hajj 2024 ta fitar a ranar Lahadi.
Shugaban hukumar Alhaji Faruku Aliyu-Enabo ya bayyana sunan marigayin da Abubakar Abdullahi wanda ya fito daga Gulma a karamar hukumar Argungu.
A cewar Aliyu-Enabo, Abdullahi ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa Gwamna Nasir Idris ya nuna alhininsa kan rasuwar tare da yi wa marigayin addu’a, inda ya roki Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi Jannatul Firdaus.
“Gwamnan ya kuma bukaci iyalan mamacin da abokan arziki da mahajjatan Kebbi da su jajirce wajen karbar nufin Allah Madaukakin Sarki cikin aminci,” i...