Tauraruwar Fina-finan Hausa, Fati Washa kenan a kasar waje inda take yawon shakatawa.
Ta saka hotunan a shafinta na sada zumunta.
Da yawa sun yaba mata inda daya daga cikin masoyanta ya bayyana cewa duk wanda ya bata shawarar ta daina Bleaching ya bata shawara me kyau.
Kuskure Ne Yi Wa Mahaifiyar Rarara Mummunar Fata Don Ta Fada Hannun 'Yan Binďiģa, Saboda Kaddara Ce Tana Iya Fadawa Kan Mahaifiyar Kowa, Cewar Wannan Malamin Addini
Shehin Malamin ya kara da cewa yana mamakin yadda bambancin siyasa ya sa musulmai suke farin ciki idan iftila'i ya fadawa abokin hamayyar su a siyasa.
Me za ku ce?
Rahotanni sun bayyana cewa, awanni 24 bayan yin garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu, Rarara har yanzu, ba'a gano inda take ba.
Kakakin 'yansandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa an kama mutane 2 da ake zargin suna da hannu a yin garkuwa da mahaifiyar Rarara din amma har yanzu ba'a gano inda take ba.
Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan Bindigar da suka je yin garkuwa da mahaifiyar Rarara sun je ne a kafa tike da muggan makamai suka shiga gidanta suka kamata.
Rahoton yace Bata musu gaddama ba kuma babu wanda ya tunkaresu saboda muggan makaman da suke dauke dasu.
Daily Trust tace ta nemi jin ta bakin Rarara amma bata yi nasara ba saboda wayoyinsa duk a kulle kuma an aika masa da sakon waya amma bar bayar da amsa ba.
Jarumar fina-finan Kannywood, Amal Umar ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu mutane na yaɗa mummunar fahimtarsu game da halayen wasu jaruman shirya fina-finan.
Amal Umar -wadda ta bayyana hakan cikin shirin Mahangar Zamani na BBCHausa - ta ce babban takaicinta shi ne yadda ake yi wa ƴan fim kallon marasa tarbiyya.
Duk da cewa akwai labarai marasa daɗi da ake yaɗawa game da masu sana’ar fim, jarumar ta nesanta kanta daga dukkan zarge-zargen da al'umma ke yi wa 'yan fim.
‘’Kowa ba ya yi mana zaton alkahiri, sai dai ki ji ana karuwai ne su, ba su kwana a gidajensu, sun raina iyayensu, irin waɗannan abubuwan, amma ni na sani, kuma masu mu’amula da ni sun sani, duk daren duniya idan na gama abin da nake yi sai na kwana a gidanmu’’, in ji jarumar.
Sauran baƙin da shir...
SHEKARA 16 DA AURE BATARE DA YAJI BA BALLE SAKI.
Darakta a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood Hassan Giggs sun cika shekara 16 da aure shi da matarsa, Jarumar Kannywood Muhibbat Abdussalam tare da samun ƙaruwar arziƙin ƴaƴa mata 3 kamar yadda kuke gani cikin wannan hoto.
Sun rayu tsawon waɗannan shekaru batare da yaji ba balle saki. Wannan gagarumin abin alfahari ne a masana'antar Kannywood.
Muna musu fatan alkhairi Allah Ya ƙara musu aminci da zaman lafiya cikin so da ƙaunar juna mai ɗorewa.
Wane fata zaku yi musu?