Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wadannan hotunan inda ta ci kwalliyar Sallah tare da kawayenta.
Hadiza ta wallafa hotunan a shafinta na sada zumunta inda masoyanta da yawa suka yaba.
Rahotanni sun bayyana cewa, Rahama Sadau ta sa an saki Zaharaddeen Sani daga wajan 'yansanda bayan da Hadiza Gabon tun a farko tasa aka kamashi.
Yanzu haka dai rahotanni sun ce Zaharaddeen Sani na gida.
Tun farko dai Hadiza Gabon ce tace matan da basu shiga fin ba kada su shiga, inda Zaharaddeen ya mata martani me zafi.
Da alama, Hadiza Bata ji dadin martanin Abokin sana'arta ba inda tasa aka kamashi.
DA ƊUMI-ƊUMI: Jarùmar Kannywood Hadiza Gabon Tasa An Kama Jarumi Zahraddeen Sani.
Hadiza Aliyu Gabon ta sa an kama jarumi Zaharaddeen sani a jihar Kaduna, rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka suna can Police Station a na kan tattaunawa.
Kamun dai ya biyo bayan kalaman da yayi a wani martani ga Hadiza Gabon inda ya ce, daga kan su Hadiza aka fara zagin ƴan masana’antar kannywood saboda shigar da sukeyi da mu’amalarsu da wasu dake wajen masana’antar ta kannywood.
Me zaku ce?
Duk Macen Dake Son Shiga Harkar Fim Din Hausa Ta Yi Hakuri Ta Je Ta Yi Aure Na Cikin Kannywood Din Ma Fata Muke Su Samu Maza Su Yi Aure, Cewar Abubakar Maishadda.
Me za ku ce?