Wednesday, January 15
Shadow

Kano

Ji yanda ta kaya bayan da gwamna Abba yace a rushe gidan Nasarawa da Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki

Ji yanda ta kaya bayan da gwamna Abba yace a rushe gidan Nasarawa da Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki

Kano, Siyasa
A jiyane dai rahotanni suka bayyana cewa, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin rushe fadar Nasarawa wadda sarki Aminu Ado Bayero ke ciki da nufin gyarata. Saidai tuni jami'an tsaro sukawa fadar kawanya dan hana aiwatar da wannan umarni. A jiyandai, Tuni har an kai motocin dake rushe gida fadar ta Nasarawa amma lamarin bai tabbata ba. Tun a jiyan dai, Wasu masu sharhi akan al'amuran yau da kullun ke ganin cewa, wannan umarni kuskurene saboda ba'a kammala shari' ba. Daya daga cikin masu irin wannan ra'ayi shine, Salihu Tanko Yakasai wanda yace gwamnan zai saka ai masa dariya saboda wannan umarni da ya bayar: https://twitter.com/dawisu/status/1803884035124474006?t=sGU-jQHoxSU0qi4uYksphQ&s=19 Wannan hukuncin kotu dai ya kawo rudani a Kano inda kowane...
YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano Ta Umarci ‘Yan Sanda Da Su Fitar Da Aminu Ado Bayero Daga Gidan Sarki Na Nassarawa dan rusheshi a gina wani

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano Ta Umarci ‘Yan Sanda Da Su Fitar Da Aminu Ado Bayero Daga Gidan Sarki Na Nassarawa dan rusheshi a gina wani

Kano
YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano Ta Umarci 'Yan Sanda Da Su Fitar Da Aminu Ado Bayero Daga Gidan Sarki Na Nassarawa dan rusheshi a gina wani. Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce za ta fara aikin rushe katangar gidan Sarki na Nasarawa da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ke ciki, tana mai cewa "saboda ya lalace". Gwamnatin ta kuma umarci kwamishinan 'yansandan jihar da ya fitar da Aminu Ado daga gidan bayan hukuncin kotu a yau Alhamis, wanda ta yi iƙirarin cewa ya ba ta nasara a kan ɓangaren da suka shigar da ƙarar. Kwamashinan Shari'a na Kano Haruna Isa ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a gidan gwamnati, inda ya jaddada cewa bangon ƙaramin gidan sarkin da ke ƙwaryar birnin Kano ya lalace. "Mun kammala shirye-shirye domin rushewa da kuma sake gi...
Ji Abinda dan gidan Sarki Muhammad Sanusi II, Adam Sanusi yace bayan hukuncin kotu a yau wanda ya jawo cece-kuce

Ji Abinda dan gidan Sarki Muhammad Sanusi II, Adam Sanusi yace bayan hukuncin kotu a yau wanda ya jawo cece-kuce

Kano
Dan gidan me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, Adam Muhammad Sanusi wanda aka fi sani da Ashraf ya bayyana godiya ga Allah bayan hukuncin kotu a yau. https://twitter.com/Adam_L_Sanusi/status/1803838627111199087?t=kdRE0ZRuHq-RtRIePMxwNg&s=19 Kotu dai ta soke sabuwar dokar data soke sabbin masarautun Kano wanda lamarin ya kawo rudanin fahimta tsakanin masoyan Sarki Muhammad Sanusi II da Masoyan Sarki Aminu Ado Bayero. https://twitter.com/Adam_L_Sanusi/status/1803793847878574563?t=D9YU71bHREHJIdEAO8lqjw&s=19 Ya kara da cewa babansa, Watau sarki Sanusi yana nan dai kuma shine me gaskiya.
Bidiyo da Hotuna Da Duminsu: Harin ‘Yan Ďabà A Kano Ya Yi Silar Muťùwàr Mutum Daya Tare Da Raunata ‘Yan Sanda Biyu

Bidiyo da Hotuna Da Duminsu: Harin ‘Yan Ďabà A Kano Ya Yi Silar Muťùwàr Mutum Daya Tare Da Raunata ‘Yan Sanda Biyu

Kano, Tsaro
Harin 'Yan Ďabà A Kano Ya Yi Silar Muťùwàr Mutum Daya Tare Da Raunata 'Yan Sanda Biyu. Dama dai wasu na kokawa da cewa an jibge 'yan daba a fadar Sarkin Kano dake Kofar kudu inda wasu ke ganin hakan ka iya zama barazanar tsaro ga al'ummar dake kewaye da yankin. https://twitter.com/Musaddiqww/status/1803537550876815767?t=zFtVr6QilV2yJF7TI9xRQQ&s=19 An dai jawo hankalin jami'an tsaro kan wannan lamari: https://twitter.com/Musaddiqww/status/1803678430346530884?t=ARnpwjVzoX22x5VVfi-_sA&s=19 Jihar Kano dai ta kasance cikin rashin tabbas akan rikicin masarautar jihar tsakanin Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero.
Kalli Bidiyon yanda aka kulle Gidan Dabo

Kalli Bidiyon yanda aka kulle Gidan Dabo

Kano
Rahotanni sun bayyana cewa wai an kulle gidan Dabo. Wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta ne ke wannan ikirari. https://twitter.com/Musaddiqww/status/1802438326735225133?t=uX0ExUbfDMFQ4drut1mL-g&s=19 Bidiyon ya nun kofar fadar sarkin Kano a Kulle. Lamarin dai ya jawo cece-kuce.
Bidiyo: Yadda Kanawa suka yiwa Gwamna Abba Kabir ihun bamayi a hanyarsa ta zuwa sallar Idi

Bidiyo: Yadda Kanawa suka yiwa Gwamna Abba Kabir ihun bamayi a hanyarsa ta zuwa sallar Idi

Kano
Rahotanni da bidiyo sun yo ta yawo kan Yadda Kanawa suka yiwa Gwamna Abba Kabir ihun bamayi a hanyarsa ta zuwa sallar Idi. Lamarin bai zo da mamaki ba ganin lamuran da suka faru a jihar ta Kano daga Chanja sarki wanda baiwa masu son Aminu Ado Bayero dadi ba zuwa rusau. https://twitter.com/Ahmad_Gogel/status/1802299626822811767?t=CZUUWUSeyPciG5gkc4w_VQ&s=19 An yi rusau din shaguna da yawa ana kwanaki 4 kamin Sallah a IBB wanda har ya jawo Wasu 'yan kasuwar suka yi zanga-zanga. Wannan dai ka iya zamarwa gwamnatin Abba Kabir Yusuf kalubale.
Kwamishinan ‘Yan Sanda Ba Shi Da Hurumin Hana Gudanar Da Bukukuwan Sallah A Kano, Cewar Gwamnatin Kano

Kwamishinan ‘Yan Sanda Ba Shi Da Hurumin Hana Gudanar Da Bukukuwan Sallah A Kano, Cewar Gwamnatin Kano

Kano
Kwamishinan ‘Yan Sanda Ba Shi Da Hurumin Hana Gudanar Da Bukukuwan Sallah A Kano, Cewar Gwamnatin Kano Daga Muhammad Kwairi Waziri A wata sanarwa da kwamishinan shari'a na jihar Kano Alh Haruna Dedari ya fitar. Inda yake cewa Kwamishinan 'yan sandan yana karbar umarni ne daga sama ba daga wajen gwamnatin jihar ba, sannan kuma ba tare da neman shawara da babban jami’in tsaro na jihar ba ko amincewar kwamitin tsaro na jihar kuma ya bayar da umarnin dakatar da bukukuwa sallah a jihar Kano ba tare da yawun Gomnatin jihar ba. Tambaya ta anan shi wanene ke ingiza Kwamishinan ’yan sandan Jihar ya kwace ikon da Gwamna yake dashi a jihar sa ?
‘Yan kasuwa a Kano sun yi zanga-zangar rushe shaguna 5000 a IBB

‘Yan kasuwa a Kano sun yi zanga-zangar rushe shaguna 5000 a IBB

Kano
A ranar Alhamis, 'yan Kasuwa a Kano sun yi zanga-zangar rushe shaguna 5000 a IBB way. An yi rusau dainne ranar Laraba bayan cikar wa'adin awanni 48 da aka baiwa masu shaguna su kwashw kayansu kuma su tashi. Da yawa cikin wadanda lamarin ya shafa aun zauna a wajan inda suka ce ba zasu tashi ba inda kuma suka rika zagin gwamnatin jihar ta Kano. Shuwagabannin kasuwar sunce sun shafe shekaru 18 suna zaune a wannan kasuwa tun bayan da aka basu wajan ta hannun Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim Rusau din ya zo kwanaki 4 kamin sallah a yayin da mutane ke rububin sayayyar sallah.
Kotu na da hurumin sauraron ƙara kan masarautar Kano

Kotu na da hurumin sauraron ƙara kan masarautar Kano

Kano
Wata babbar kotu a Kano ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar kan rikicin masarautar Kano, musamman kan abin da ya shafi kare hakkin ɗan'adam bisa dogaro da sashe na 46 na kundin tsarin mulkin Najeriya. Alƙalin kotun, mai shari’a Liman Mohammed na babbar kotun tarayya da ke jihar, ya yanke hukuncin cewa tsohon sarki Aminu Ado Bayero na da damar a saurare shi a kotu. Sai dai alkalin ya ce ba magana ce a kan cancantar majalisar dokokin jihar na sauya dokar masarautun jihar ko kuma a'a ba. Alƙalin ya bayyana cewa kotun ba ta ƙalubalantar damar da gwamnatin jihar ke da shi na naɗawa ko sauke sarki. A ranar 23 ga watan Mayu ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, bayan majalisa ta amince da ita. Wann...