Monday, January 13
Shadow

Amfanin Kankana

Amfanin bawon kankana a fuska

Amfanin Kankana
Ba sha a ji dadi a baki bane kadai amfanin Kankana, yana kuma da amfani masu yawa a jikin dan Adam musamman a fuska. A wannan rubutu, zamu muku bayanin Amfanin bawon Kankana a fuska. Bawon kankana idan aka shafashi a fuska yana sanya fuskar ta yi haske. Hakanan kuma yana maganin abubuwan dake sa fuska ta tattare ta yi kamar ta tsaffi da kuma duhun da hasken rana ke sa fuska. Amfani da bawon kankana ko kankanar kanta ko man shafawa da aka hada da kankana na taimakawa matuka wajan zaman fuska tana sheki irin ta matasa. Hakanan ruwan kankana ko lemun da aka hada da kankana idan aka shafashi a fuska akai-akai, yana taimakawa wajan kawar da kurajen fuska. Shafa ruwan kankana a fuska yana kawar da tabon bakaken abubuwan dake fuska masu kama da kuraje sannan yana hana sake fito...

Amfanin kankana ga mace

Amfanin Kankana
Kankana na da matukar amfani sosai a jikin dan Adam musamman mata. A wannan rubutu, zamu bayyana amfanin Kankana a jikin mata. Da farko dai kankana na da Sinadaran Vitamins A, B6, da C wanda suke karawa fata sheki, da lafiya. Hakanan tana maganin bushewar fata, da maganin ciwon daji watau Cancer. Ga mata masu ciki, Kankana na taimakawa sosai wajan nakuda da hana bari da haihuwar bakwaini. Kankana na daya daga cikin kayan itatuwan da masana ilimin kimiyyar lafiya ke cewa mace me neman daukar ciki ta ci dan samun ciki cikin sauri.

Amfanin kankana ga namiji

Amfanin Kankana
Kankana na daya daga cikin kayan marmari da ake amfani dasu a kasar Hausa, a wannan rubutun, zamu kawo muku jawabin amfanin Kankana ga Namiji. Kankana na taimakawa maza wajan lafiyar gabansu musamman maraina ga mazan da suka fara manyanta. Tana da sinadaran Antioxidant wanda ke boye alamun tsufa. Tana kara gudun jini a jikin mutum wanda hakan zai karawa namijin dake shanta karfin Azzakari. Masana sunce ga maza wanda suka manyanta wanda ke amfani da maganin karfin maza dan Azzakarin su ya tashi, zasu iya yin amfani da kankana a madadin shan wadannan magunguna. Kankana na taimakawa wajan samun ingantaccen bacci. Kankana na taimakawa maza wajan kara ingancin maniyyinsu. Kankana na taimakawa karin lafiya ga zuciya. Kankana na kuma da sinadaran dake yaki da cutar Daji w...