Maganin kaikayin dubura
Akwai maginin likita na kaikayin Dubura sannan akwai dabarun da mutum zai yi a gida dan magance wannan matsala.
A wannan rubutu, zamu bayyana dabarun da za'a iya amfani dasu ne a gida dan magance wannan matsala.
Hanya ta farko ta magance kaikayin dubura shine a tabbatar ana wanke jiki da kyau idan an kammala yin kashi.
Kada a sa sabulu me kanshi ko a shafa mai ko turare a wajan, kada a goge wajan da tsumma me kaushi, a wanke da ruwa kadai ya wadatar.
Idan an ji kai kayi, a daure kada a sosa, sosa kaikayin dubura zai iya maka dadi ko ka dan ji saukin abin na dan lokaci amma abinda yafi shine kada a sosa. Idan abin yayi yawa, ana iya yin wana da ruwan dumi dan samun sauki.
A gujewa saka kaya masu matse jiki da zasu iya shiga tsakanin mazaunan mutum su makale, hakan zai karawa ...