Monday, January 13
Shadow

Nakuda

Alamomin nakuda

Haihuwa, Nakuda
Akwai alamomin nakuda da yawa, ga wasu daga cikinsu kamar haka: Jin matsewa a gabanki, zai rika matsewa yana budewa. Zaki rika jin shi kamar lokacin da kike jinin al'ada. Yayin da ruwa me kauri ya zubo daga gabanki. Ciwon baya. Jin kamar zaki yi kashi wanda hakan yana faruwane saboda yanda kan danki ke shirin fitowa waje. Da kin fara jin wannan alamomi to a garzaya a tafi Asibiti ko a kira ungozoma. Sauran Alamomin sun hada da zubar da jini. Abin cikinki ya daina motsi sosai.

Cikin wata hudu

Haihuwa, Lauyayin ciki, Nakuda
Bayan cikinki ya kai wata 4, ga abubuwan dake faruwa: Dan dake cikinki ya kai girman inchi 3 ko ace 8 cm. Za'a iya gane wane jinsi ne abinda ke cikinki saboda za'a iya ganin al'aurarsa a na'urar gwaji ta Ultrasound. Gashin kan abinda ke cikinki ya fara fitowa. An halicci saman baki ko lebe. Da yawa daga cikin Alamomin farko da kika fara ji na daukar ciki zasu daina damunki bayan da cikinki ya kai watanni 4. Saidai matsalolin rashin narkewar abinci zasu iya ci gaba da bayyana a jikinki, kamar wahala wajan yin kashi, zafin kirji ko zuciya. Nononki zai kara girma, zai rika zafi sannan kan nononki zai kara yin baki. Zaki iya samun matsalar numfashi sama-sama ko kuma yinshi da sauri. Dasashin bakinki zai iya yin jini, zaki iya yin habo, watau zubar da jini ta hanci, ...

Cikin wata biyar

Gwajin Ciki, Haihuwa, Nakuda
Duk da yake cewa kowace mace da irin yanda ta ke daukar cikinta amma a wata 5 da daukar ciki, za'a ga girman cikinki ya bayyana. Jikinki zai fara canjawa yana daidaituwa da yanda cikinki ke kara girma. Ga wasu alamu da ke nuna cewa cikinki ya kai wata 5: Kafafunki zasu Kumbura: saboda nauyin da kika kara saboda cikin dake jikinki, kafafunki zasu iya kumbura, kwanciya a daga kafa sama yana taimakawa wajan magance wannan matsala. Ciwon kwankwaso: Saboda yanda cikinki ke fitowa, bayanki zai rika shigewa ciki wanda hakan zai iya kawo miko ciwon kwankwaso. Juwa: A yayin da jaririnki ya ke girma, yawan jinin dake gudana musamman zuwa kanki zai iya raguwa wanda zai sa ki ji juwa. Mura: Zaki iya fuskantar Mura, hancinki ya toshe ko kuma yayi ta yoyo, kai yana ma iya fitar da jini...

Alamun ciki yakai haihuwa

Haihuwa, Nakuda
Akwai alamu da yada dake nuna ciki ya jai haihuwa: Zaki iya jin zafi sosai kamar na lokacin al'ada. Zaki ji mahaifar ta matse sannan zata saki. Hakan zai iya ci gaba da faruwa, yana zuwa yana tafiya duk bayan mintuna 5, kuma lokaci na tafiya hakan na kara tsananta. Da kinji haka to a kira ungozoma ko kuma a kaiki asibiti, Haihuwa ta zo. Zaki iya jin ciwon baya sosai. A yayin da kike da ciki, wani ruwa me yauki yana taruwa ya kulle kofar mahaifarki, to a yayin da kika zo haihuwa, wannan ruwan zai fito waje, idan kika ganshi, me yauki ne kuma Pink to haihuwa ta zo, saidai wasu na haihuwa ba tare da ganin ruwan ba. Amma masana kiwon lafiya sun ce rashin ganin ruwan ka iya zama alamar cewa akwai matsala tare da ke ko abinda zaki haifa. Dan haka ya kamata a nemi ungozoma ko...