Tuesday, January 14
Shadow

Labaran Manchester United

A wannan satin ake sa ran Manchester United zata kori Ten Hag

A wannan satin ake sa ran Manchester United zata kori Ten Hag

Kwallon Kafa, Labaran Manchester United
A wannan satin da muke ciki ake sa ran Kungiyar Manchester United zata kori me horas da 'yan wasanta Erik Ten Hag. Thomas Tuchel ne dai ake tsammanin zai maye gurbin Ten Hag a matsayin sabon kocin United. Tuni kuma har Thomas Tuchel ya gana da wakilin Manchester United, Sir Jim Ratcliffe Tuchel ya bayyana cewa idan aka bashi aikin horas da Manchester United, zai dawo da Jadon Sancho zai kuma yi aiki da Mason Mount.
Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya

Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya

Casemiro, Labaran Manchester United
A wani abin ban mamaki, dan kwallon tsakiya na Manchester United, Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya. Hakanan bayan zuba hannun jarin, a yanzu ya shiga cikin daraktoci masu gudanarwa na kungiyar. Akwai dai tantamar ci gaba da zaman Casemiro a Kungiyar Manchester United indaa ake alakantashi da barin kungiyar. A ranar 3 ga watan Yuni dai an ruwaito cewa, Cristiano Ronaldo ya nemi Casemiro ya koma kungiyar Al nassr su yi wasa tare. Hakanan akwai kungiyoyin Al ahli dana Alqasidiya da suma ke zawarcin Casemiro.