Wednesday, January 15
Shadow

Labaran Falasdinawa

Masu zanga-zanga sun yi artabu da ƴan sandan Isra’ila

Masu zanga-zanga sun yi artabu da ƴan sandan Isra’ila

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Siyasa, Yakin gaza da isra'ila
Masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati sun yi taho mu gama da ƴan sanda, a daidai lokacin da ake gangamin a sassan Isra'ila kan kiran a kuɓutar da sauran waɗanda ke hannun Hamas. Sai dai mai magana da yawun sojin ƙasar,Rear admiral Daniel Hagari ya ce su na ƙoƙari kan batun. Ya ce dakarun Isra'ila sun ɗauki makwanni su na shirye-shiryen aikin nan, an ba su horo kan yadda za su kuɓutar da mutanenmu, ba za mu gaji ba har sai sauran sun dawo. Masu zanga-zangar su na sukar firaiminista Benjamin Netanyahu, wanda ke ganawa da iyalan waɗanda aka saka maimakon waɗanda ke cikin tashin hankali da rashin tabbacin ko nasu ƴan uwan za su dawo gida a raye.
Majalisar Dinkin Duniya ta saka Kasar Israela cikin masu kisan kananan yara

Majalisar Dinkin Duniya ta saka Kasar Israela cikin masu kisan kananan yara

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Siyasa, Yakin gaza da isra'ila
Majalisar Dinkin Duniya ta saka kasar Israela cikin kasashe masu kisan kananan yara. Hakan ya biyo bayan kisan sa kasar kewa Falas-dinawa a zirin gaza. Wakilin Israela a Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan ne ya bayyana haka. Inda yace an sanar dashi matakinne ranar Juma'a. Hakanan ministan harkokin kasashen waje na kasar Israela, Katz ya bayyana cewa, zasu dauki mataki kuma wannan abu da majalisar ta yi zai canja dangantakar dake tsakaninsu da Israela.
Ji matakin da Kasar Iran tace zata dauka akan kasar Israela bayan da Israelan ta sake kai harin da ya kashe sojan Iran din

Ji matakin da Kasar Iran tace zata dauka akan kasar Israela bayan da Israelan ta sake kai harin da ya kashe sojan Iran din

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
A jiyane dai muka samu rahoton cewa, kasar Israela ta kai wani mummunan hari a garin Aleppo dake kasar Syria wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa ciki hadda me baiwa kasar Iran shawara akan harkar soji. A martanin kasar Iran kan harin, Kwamandan dakarun IRGC na kasar Salami ya bayyana cewa, Israela ta saurari harin ramuwar gayya. A baya dai, irin wannan harin ne Israela ta kai kan ginin ofishin jakadancin Iran wanda ya kashe wasu janarorin soja na Iran. Hakan yayi sanadiyyar harin ramuwar gayya akan Israela da Iran ta yi wanda ya baiwa Duniya mamaki kuma ya tayar da hankalin kasar Israela. A wannan karin dai ba'a san wane irin harin ramuwar gayyane Iran zata kai akan Israela ba.
Kuma dai: Kasar Israela bata daddara ba, ta sake kai harin da ya kashe sojan kasar Iran

Kuma dai: Kasar Israela bata daddara ba, ta sake kai harin da ya kashe sojan kasar Iran

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Tsaro, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Israela ta kai wani mummunan hari a birnin Aleppo na kasar Syria da kashe mutane da yawa ciki hadda wani sojan kasar Iran. Saidai zuwa yanzu, kasar ta Israela bata kai ga bayyana cewa itace ta kai harin ba. Wannan ne dai hari na farko tun bayan na 1 ga watan Afrilu wanda Israelan ta kai kan babban birnin Syria, Damascus wanda yayi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar Iran. A wancan lokaci dai, kasar Iran din ta mayar da martani ta hanyar jefawa kasar Israela makamai da yawa wanda sai da kasashen Amurka, ingila da Faransa suka taru suka taresu. Wannan karin kuma ba'a san wane mataki ne kasar Iran din zata dauka akan wanan harin da Israelan ta kai mata ba.
Kasar Yahudawan Israela ta ce ‘yan kasarta su fice daga kasar Maldives bayan da ta haramtawa Yahudawan shiga kasarta saboda kisan da sukewa Falas-dinawa

Kasar Yahudawan Israela ta ce ‘yan kasarta su fice daga kasar Maldives bayan da ta haramtawa Yahudawan shiga kasarta saboda kisan da sukewa Falas-dinawa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kasar Maldives ta hana Yahudawan Israela shiga kasarta saboda kisan da Israela kewa Falas-dinawa. Shugaban kasar, Mohamed Muizzu ne ya bayyana hakan a ranar Litinin. Jimullar Yahudawan Israela dubu 11 ne suka je kasar ta Maldives yawom shakatawa a shekarar data gabata. A matsayin martani ga wannan matakin na kasar Maldives, ministan harkokin kasashen waje na Israelan Israelan Oren Marmorstein yace duk 'yan kasarsu da suke kasar ta Maldives su fice.
A karshe dai, ba dan yana so ba, Shugaban Israela, Benjamin Netanyahu ya amince da Tsagaita Wuta akan Falas-dinawa bayan Tursasawar kasar Amurka

A karshe dai, ba dan yana so ba, Shugaban Israela, Benjamin Netanyahu ya amince da Tsagaita Wuta akan Falas-dinawa bayan Tursasawar kasar Amurka

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban Israela, Benjamin Netanyahu ya amince da tsagaita wuta akan Falas-dinawa bayan tursasawar kasar Amurka. Rahoton yace, Israela ta amince da tsagaita wutarne a Yau, Lahadi. A ranar Juma'ar data gabata ne dai Shugaba Biden ya gabatar da tsarin na tsagaita wuta wanda Benjamin Netanyahu yayi watsi dashi. Saidai a yau ya amince. Hakanan akwai rahotannin dake cewa, itama kungiyar Hamas ta amince da tsarin, amma bata sanar da hakan a hukumance ba. Me baiwa Benjamin Netanyahu shawara kan harkokin kasashen waje, Ophir Falk ne ya bayyana hakan inda yace ba shiri bane me kyau amma suna son kubutar da duka mutane su dake hannun Hamas shiyasa suka amince dashi. Saidai ya nanata aniyarsu ta son ganin bayan kungiyar ta Hamas.
Tsagaita wuta a Gaza: Ministocin Isra’ila sun yi barazanar ficewa daga gwamnatin Netanyahu

Tsagaita wuta a Gaza: Ministocin Isra’ila sun yi barazanar ficewa daga gwamnatin Netanyahu

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Wasu Ministocin Isra’ila biyu masu tsatsauran ra’ayi sun yi barazanar ficewa daga gwamnatin hadin gwiwar ƙasar idan har Benjamin Netanyahu ya amince da tayin sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da shugaba Biden na Amurka ya gabatar. Yarjejeniyar da Mista Biden ya sanar ta samu karɓuwa daga ɓangaren ƴan adawa a Isra’ila da ƙasashe masu shiga tsakani. A ranar juma'a ne shugaba Biden ya yi tayin tsagaiwa wutar ta hanyar bullo da matakai uku, da suka haɗa da tsagaita wuta na mako shida a matakin farko. Tare da janyewar dakarun Isra'ila daga wurare masu yawan jama'a a Gaza. Sannan ya ce yarjejeniya za ta bayar da damar sakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su da kuma tsagaita wuta na dindin tare da sake gina Gaza. To sai dai ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben-Gvir, ya ce duk wa...
Kasar Maldives ta haramtawa Yahudawan Israela shiga kasarta saboda kisan Falasdinawa

Kasar Maldives ta haramtawa Yahudawan Israela shiga kasarta saboda kisan Falasdinawa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kasar Maldives ta zama ta farko data hana mutanen kasar Israela shiga kasarta saboda kisan da sukewa Falas-dinawa. Yakin da kasar Israela take yi da Falasdinawa dai ya fara jawo mata Allah wadai har ma daga manyan kasashe. Kasa ta baya-bayannan data dauki mataki akan kasar Israela itace kasar Faransa wadda ta hana kasar ta Israela halartar taron bajakolin makamai mafi girma a Duniya.
Kalli Kuga: Kungiyar Hezbollah ta sanar da lalata babban makamin kasar Israela me suna Iron Dome da take amfani dashi wajan tare makaman da ake harba mata

Kalli Kuga: Kungiyar Hezbollah ta sanar da lalata babban makamin kasar Israela me suna Iron Dome da take amfani dashi wajan tare makaman da ake harba mata

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta sanar da kaiwa babban makamin da kasar Israela take ji dashi wajan tare makaman da ake aika mata me suna Iron Dome. Hezbollah tace ta aikawa Iron Dome bamabamai ne wanda ya lalatashi da kuma kashe ko kuma raunata sojojin dake kula dashi.
Amurka za ta tallafa don sake gina makarantu da asibitoci a Gaza – Biden

Amurka za ta tallafa don sake gina makarantu da asibitoci a Gaza – Biden

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ana bukatar hanyar sasanci domin kawo karshen yakin yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da daidaita lamurra a kan iyakar arewacin Lebanon. Mista Biden ya ce akwai bukatar shugabannin Falasdinawa da na Isra'ila su hada kai domin sake gina Gaza, ta yadda ba za a bar Hamas ta sake mallakar makamai ba. ''Amurka za ta tallafa wajen sake gina makarantu da asibitocin Gaza'', in ji Biden. Ya kara da cewa shirin zai taimaka wajen sake daidaita lamurran dangataka da Saudiyya da magance barazanar Iran a yankin. Mista Biden ya kuma gabatar da kudurin da zai bai wa Isra'ila damar zama mai karfi a yankin.