Wednesday, January 15
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba>>Gwamnoni

Gwamnonin jihohin kasar nan 36 sun ki amincewa da tayin Naira dubu 60 mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta ga.

Daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, Hajiya Halimah Salihu Ahmed ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau Juma’a.

A tuna cewa a ranar Litinin ne kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, TUC, suka shiga yajin aikin sai baba-ta-gani bayan sun ki amincewa da tayin N60,000 da gwamnatin tarayya tayi a matsayin mafi karancin albashi.

Amma daga baya sun sanar da cewa za su sassauta yajin aikin na tsawon mako guda domin ba da damar tattaunawa da gwamnatin tarayya, wadda ta yi alkawarin kara albashin daga N60,000.

Karanta Wannan  Muna Maraba da Kwankwaso ya zama mataimakin Obi>>Inji Jam'iyyar Labour party

Sai dai gwamnonin sun ce mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 60 ba mai yiwuwa ba ne, kuma ba zai dore ba, suna masu cewa idan aka aiwatar da shi, hakan zai sa wasu jihohin kasar nan su rika karbar bashi domin biyan albashin ma’aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *