Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: A karo na biyu, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace ba fa zai ci gaba da ganin cin kashin da akewa Kiristoci a Najeriya ba sai ya kawo musu dauki

Donald Trump ya jaddada cewa Amurka za ta iya tura dakaru Najeriya ko kuma kaddamar da hare-hare domin hana abin ya kira kisan Kiristoci da ake yi.

Ya shaida wa manema labarai cewa ba zai bari a ci gaba da kisan ba.

“Ana kashe kiristoci da dama a Najeriya kuma adadi da yawa, ba zan bari a ci gaba ba.” in ji Trump.

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi maraba da samun hadin kan Amurka wajen yaƙi da mayaka masu tsattsaran ra’ayin addini tare da musanta cewa mayakan sun fi kashe kiristoci.

A watan da ya gabata Amurka ta saka Najeriya cikin jerin kasashen da take da damuwa da su kan take ƴancin addini.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Malmin Imamu Malik Dan Shi'ane sannan Turawan Ingila ne suka kawo Wahabiyanci dan raba kan Musulmai >>Inji Malam Nura Khalid

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar, Mista Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkaɓe abin da ya kira ƴanta’adda masu kishin Islama da ke aikata ta’asa.

Ya kuma yi barazanar dakatar da duk wani taimakon Amurka ga Najeriya.

Tuni Najeriya ta yi watsi da ikirarin cewa ana kashe kiristoci ba gaira ba dalili a yankin arewacin inda galibi musulmi suka fi yawa.

A bayanin da Mista Trump ya wallafa a kafar sadar zumuntarsa ta Truth a ranar Asabar ya ce ya ba ma’aikatar tsaron Amurka umarnin ta fara shirin ɗaukar mataki kan Najeriya – “Idan har gwamnatin Najeriya ta bari ana ci gaba da kashe Kirista,” in ji shi.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Nan Yaran Da Aka Sako Daga Gidan Yari Ne A Jiya Suke Kwasar Girki

Shugaban wanda ke ɗa’awar samun lambar yabo ta zaman lafiya a duniya ya kuma yi mummunan kalamai ga Najeriya inda ya ce “Amurka za ta shiga cikin ƙasar da a yanzu ta wulakanta.”

Tun a ranar Juma’a Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa “ana kashe dubban kiristoci a Najeriya kuma masu tsattsauran ra’ayin Islama ne ke da alhakin kisan,” ba tare da ya bayar da wata hujja ba.

Wasu yansiyasar Amurka ne suka fara hura wutar zargin inda a watan Maris ɗanmajalisar Amurka Chris Smith ya yi kiran a saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake da damuwa a kansu.

Haka ma a watan Oktoba Sanata Ted Cruz da ɗanmajalisar wakilai Riley Moore dukkaninsu ƴan Republican suka zargi gwamnatin Najeriya da yin ko oho da kisan da ake yi wa kiristoci.

Karanta Wannan  Kalli hotuna da Bidiyo: Yanda mata suka cire kayansu suka yi zanga-zanga tsirara

Wannan matakin ya ƙara wa masu da’awar ana kashe kiristoci ƙwarin guiwa a Najeriya tare da ƙara ingiza su a kasar da ta yi fama da rikicin ƙabilanci da na addini a baya da kuma ke ci gaba da tasiri a wannan zamanin na tsarin siyasa a kasar.

Najeriya dai ta tade tana fama da tashe-tashen hankula da dama wadanda masana suka ce ana kashe Kiristoci da Musulmai ne ba tare da bambancewa ba.

i

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *