
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Burkina Faso ta sako sojojin Najeriya 11 data kama a kwanakin baya biyo bayan ganawar sulhu da aka yi tsakanin wakilan gwamnatin Najeriyar dana Burkina Faso.
An sako sojojinne bayan da suka shafe kwanaki 9 a hannun kasar ta Burkina Faso.
Zagazola Makama yace wani dake da masaniya kan lamarin ne ya sanar dashi hakan.