
Bayan sallar La’asar a ranar Talata ne ake sa ran za a gudanar da jana’izar fitaccen attajirin nan Alhaji Aminu Ɗantata a masallacin Madina.
Mustapha Junaid, mataimaki na musamman ga marigayin ya shaida wa BBC cewa shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’izar.
“Alhamdu lillah an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina kuma yanzu haka za a je Shakzura inda a nan ne za a ƙarasa shirya shi kafin daga bisani a kai shi haramin Madina domin gudanar da sallah kamar yadda hukumomin Saudiyya suka amince.” In ji Mustapha Junaid.
A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.
A shekarar Hijira (ta Musulunci) kuma, ya rasu yana da shekara 97, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya shaida wa BBC.
Hamshaƙin attajirin ya rasu ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya, kamar yadda wani ɗansa ya shaida wa BBC.
Bayanai sun nuna cewa marigayin ya sha bayyana sha’awarsa cewa “Allah ka kashe ni a wannan gari” a duk lokacin da ya ziyarci garin Madina da ke Saudiyya.